Rikicin Sarauta Ya Ɗauki Sabon Salo, EFCC Ta Gayyaci Mutum 7 Su Amsa Tambayoyi
- EFCC ta gayyaci masu zaben sarki daga masarautar Oyo don amsa tambayoyi kan zargin karɓar na goro a wajen fitar da sabon Alaafin
- Rahotanni sun nuna cewa ana zargin masu zaben sun karɓi rashawa mai yawa don fifita wani ɗan takara, wanda ya ja hankalin EFCC
- Hukumar ta tabbatar da cewa bincike ya kankama kuma wasu daga cikin masu naɗin sun amsa gayyatar, sauran za su bayyana cikin makon nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Hukumar yaƙi da cin da hanci rashawa a Najeriya watau EFCC ta gayyaci masu zaben sarki su bakwai daga masarautar Oyo domin amsa tambayoyi.
EFCC ta gayyaci sarakunan waɗanda ke da alhakin zaɓen sabon Alaafin bisa zargin su da karɓar rashawa daga masu neman sarautar.
Gwamna Makinde ya kawo karshen rikicin sarauta
Wannan dai na zuwa ne bayan Gwamna Seyi Makinde ya amince da naɗin Yarima Abimbola Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo, jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Makinde ya amince da naɗin sabon sarkin ne bayan shafe shekaru biyu ana rigima kan sarautar.
Bayan haka ne aka fara zargin wasu daga cikin masu alhakin zaɓen sarkin cewa sun karɓi kuɗaɗe daga masu neman sarautar tare alkawarin za su zaɓe su.
EFCC ta gayyaci masu alhakin zaɓen Alaafin
Mai magana da yawun hukumar EFCC, Mista Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa biyu daga cikin masu zaben, waɗanda ake kira da ‘Oyomesi,’ sun amsa gayyatar.
Ya bayyana cewa sauran za su bayyana a gaban hukumar EFCC cikin makon nan domin amsa tambayoyi kan zabin sabon Alaafin.
Oyewale ya ce:
"Ina tabbatar maku da cewa muna kan bincike dangane da wannan batu. Ba mu kama wani daga cikin masu naɗin ba, mun gayyace su ne kawai. Muna sa ran sauran za su bayyana nan da mako ɗaya.”
A halin da ake ciki, wani rahoto ya yi zargin cewa EFCC ta kama wasu daga cikin masu zaben sarkin saboda zargin karɓar rashawa.
Rahoton ya ce gayyatar EFCC ta biyo bayan ƙorafin ɗaya daga cikin masu neman sarautar da ke zargin cewa masu naɗin sarkin sun karɓi ƙudi don fifita wani ɗan takara.
Jerin sarakunan da EFCC ta gayyata
Rahoton ya ambaci sunayen masu maɗin sarkin da EFCC ta gayyata kamar haka:
1. Basorun na Oyo – Mai Martaba Yusuf Ayoola
2. Agbaakin na Oyo – Mai Martaba Asimiyu Atanda
3. Samu na Oyo – Mai Martaba Lamidi Oyewale
4. Lagunna na Oyo – Mai Martaba Wakilu Oyedepo
5. Akinniku na Oyo.
Ana zargin cewa masu zaben Alaafin na Oyo sun karɓi rashawa ta miliyoyin Naira don tallafawa wani ɗan takara ya zama ssrki, hakan ya sa EFCC ta gayyace su domin bincike.
Makinde ya ba sabon Alaafin sandar mulki
A wani labarin, kun ji cewa duk da ce-ce-ku-cen da ake yi, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya miƙa sandar mulki ga sabon Alaafin na Oyo, Abimbola Akeem Owoade.
An yi wannan bikin mika sandar mulki a fadar gwamnatin Oyo da ke garin Ibadan bayan kusan shekaru uku da rasuwar tsohon Alaafin, Lamidi Adeyemi III.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng