Abba Ya Kwato Motocin da Jami'an Ganduje Suka Tsere da Su daga Kano
- Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika motoci 12 ga Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi domin saukaka jigilar daliban manyan makarantu a fadin jihar
- An gyara motocin bayan an kwato su daga hannun jami'an gwamnati da ta gabata, kuma za a rika yi wa dalibai rangwamen kashi 80% na kudin mota
- Manyan mutane da iyaye sun yaba wa kokarin gwamnan tare da yi masa addu’ar samun tazarce a wa’adi na biyu domin ci gaba da ayyukan alheri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A ci gaba da kokarinsa na inganta rayuwar dalibai a Jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samar da motoci 12 da za su saukaka jigilar daliban manyan makarantu.
Gwamnan ya mikawa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi motocin ne domin su yi aiki a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Mai magana da yawun gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook cewa matakin na cikin kokarin gwamnati na magance matsalolin sufuri da dalibai ke fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kwato motoci wajen jami'an Ganduje
A cewar kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, an kwato motocin ne daga hannun jami'an gwamnatin baya da suka yi awon gaba da su.
Bayan kwato motocin, gwamnati ta bayar da umarnin gyara su ta hannun ma’aikatar sufuri, domin tabbatar da cewa sun dawo cikin hayyacinsu..
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa;
“Mun kwato wadannan motocin, mun gyara su, kuma mun dawo da su domin taimakawa dalibanmu wajen rage matsalolin sufuri da suke fuskanta.”
Haka zalika, gwamnan ya tabbatar da cewa dalibai za su rika samun rangwamen kashi 80% na kudin mota, domin saukaka musu zirga-zirga.
Jan hankali kan amfani da motocin
Gwamnan ya gargadi masu kula da motocin da direbobi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata, domin ci gaba da amfani da su na tsawon lokaci.
Ya kuma yi kira ga dalibai su kasance masu bin doka da oda yayin amfani da motocin, tare da tabbatar da kiyaye su daga lalacewa.
“An samar da motocin nan ne ba domin wani abu ba sai amfanin ku dalibai. Saboda haka, ku bayar da gudunmawa wajen kula da su,”
- Abba Kabir Yusuf
An yi wa Abba Kabir fatan alheri
Mataimakin gwamna kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yabawa kokarin gwamna Abba Kabir Yusuf kan wannan tsari na tallafawa dalibai.
Ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi za ta yi amfani da motocin bisa yadda aka tsara, domin cimma manufar gwamnati.
Haka zalika, Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Ali Namadi Dala, ya bayyana cewa an gyara motocin yadda za su dace da matakan amfani a duniyar yau tare da tabbatar da lafiyar su.
An yi wa Abba addu'ar tazarce a 2027
A madadin iyaye, tsohon Mataimakin Gwamna kuma Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar North West, Farfesa Hafiz Abubakar ya yaba wa yunkurin gwamnan.
Farfesa Hafiz Abubakar ya ce matakin ya zo a daidai lokacin da ya dace, kuma suna addu’a Allah ya ba Abba nasara a karo na biyu domin ya ci gaba da ayyukan alheri a jihar Kano.
Abba ya yabi hadiminsa mai amana
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yaba wa hadiminsa da ya dawo da rarar kudi har Naira miliyan 100.
Rahotanni sun nuna cewa kwamitin da gwamnan ya kafa domin dinka kayan makaranta ne ya dawo da kudin bayan kammala aiki.
Asali: Legit.ng