Lokutan da Sojoji Suka Kai Hare Hare kan Mutane bisa Kuskure daga 2024 zuwa Yau

Lokutan da Sojoji Suka Kai Hare Hare kan Mutane bisa Kuskure daga 2024 zuwa Yau

  • Rundunar soji ta hallaka daruruwan fararen hula bisa kuskure a hare-haren sama da suka yi kan 'yan ta'adda a Arewacin Najeriya
  • A Zamfara, wani sabon harin jirgin sama ya hallaka mutane 20 da ke aiki da wata kungiyar tsaro, cewar gwamnatin Dauda Lawal
  • Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun nuna damuwa kan hare-haren sama da ke ci gaba da jawo asarar rayukan farar hula a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

An sha samun hare-haren sojojin sama na Najeriya da ke kashe daruruwan fararen hula bisa kuskure a Arewacin Najeriya.

Hakan ya faru saboda hare-haren sama da aka kai kan 'yan ta'adda a Arewacin Najeriya a tsawon shekaru.

Hare haren sojojin sama da ya hallaka fararen hula
An samu tsautsayi kan hare-haren sojoji kan fararen hula a kokarin hallaka yan ta'adda. Hoto: @jrnaib2.
Asali: Twitter

Yawan mutane da suka mutu a harin kuskuren Sojoji

ABC News ta ruwaito cewa yawancin wadanda suka rasa rayukansu mutane ne da aka kai wa harin bam bisa kuskure da ake zaton yan ta'adda ne.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa ya faɗawa gwamnatin Tinubu dabarar murƙushe ƴan ta'adda cikin sauƙi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aƙalla mutane 465 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru 11 da ake samun irin wannan kuskure daga jami'an tsaro, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton ya ce harin da ya fi muni shi ne wanda ya faru a Tudun Biri da ke jihar Kaduna a ranar 3 ga watan Disambar 2023.

Yayin harin, akalla mutane 120 ne suka rasa rayukansu wanda ya jawo ka-ce-na-ce daga ɓangarorin kasar baki daya da ake zargin akwai sakaci a lamarin.

Na biyunsa shi ne harin Rann da ke jihar Borno a ranar 17 ga watan Janairun 2017 inda mutane 115 suka rasa rayukansu sanadin harin.

Legit Hausa ta duba muku wasu lokuta da sojojin suka kai hari a 2024 da kuma sabuwar shekarar 2025.

1. Jihar Kaduna - Satumbar 2024

Mazauna kauyuka biyu a jihar Kaduna sun zargi jami'an sojojin saman Najeriya da kai masu hari a masallaci da kasuwa.

Kara karanta wannan

Wasu yan Kano 19 da suka je daurin aure sun kone kurmus, an ceto mutane 11

An yi zargin mutane 24 aka gano da su ka hada da manoma da yara bayan kurar harin ta lafa, lamarin da sojoji su ka musanta.

Mataimakin daraktan yada labaran rundunar, Gruf Kyaftin Kabiru Ali ya yi bayanin cewa an kai harre-haren kan yan ta'adda.

Harin sojoji ya hallaka mutane a Kaduna

2. Jihar Sokoto - Disambar 2024

Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu suka samu munanan raunuka sakamakon wani hari da jirgin yaki ya kai a karamar hukumar Silame ta Jihar Sokoto.

Lamarin, wanda ya faru a safiyar Laraba 25 ga watan Disambar 2024 da misalin karfe 7:00, ya shafi kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa da ya sanadin mutuwar mutane 10.

An kashe fararen hula bisa kuskuren harin sojojin sama

3. Jihar Zamfara - Janairun 2025

Ana fargabar mutane da dama sun mutu a wani a kauye da ake kira Kakindawa a karamar hukumar Zurmi a Zamfara.

Bayanai sun nuna ana zargin jirgin saman jami’an tsaro ya sake jefa bam wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Kara karanta wannan

"Har yanzu babu hujja," Rundunar soji ta yi magana kan kuskuren jefa bom a Zamfara

Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Janairun 2025 inda aka yi ta ce-ce-ku-ce kan lamarin wanda jami'an tsaro suka musanta tun farko.

Harin sojoji ya kashe fararen hula a Zamfara

Alkawarin gwamnatin Najeriya kan hare-haren

Gwamnatin Najeriya ta sha yin alkawarin bincikar hare-haren sama da ake ka iwa ba da gangan ba, amma galibin alkawuran basu cika ba.

Al'umma da dama suna zargin cewa akwai ganganci a hare-haren da ake kai wa yayin da yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka.

Matakan dakile hare-haren sojoji

Wasu na ganin matakin da zai taimaka shi ne horar da matuka jirgi da inganta dabarun kai hari, tare da karfafa hadin kai tsakanin sojoji da al’umma.

Ana ganin hakan zai taimaka wurin dakile rashin tsaro musamman idan aka samu hadin kan al'umma wurin ba da bayanan sirri ga hukumomi.

Gwamna Lawal ya yaba wa jami'an tsaro

Kun ji cewa bayan kai harin kuskure kan fararen hula, Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa kokarin sojojin Najeriya a sabon farmakin da suka kai kan 'yan bindiga a Jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Harin sojoji: Gwamna ya jajanta, ya yaba wa jami'an tsaro kan tarwatsa yan bindiga

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta kai harin jirgin sama kan 'yan bindiga da ke kai farmaki a Zurmi da Maradun.

Gwamnatin Zamfara ta jajanta wa iyalan jami'an JTF da aka rasa a Tungar Kara, yana tabbatar da goyon baya ga tsaro da wanzar da zaman lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.