Tinubu Ya Jaddada Shirin Ragargazar 'Yan Ta'adda a Fadin Najeriya

Tinubu Ya Jaddada Shirin Ragargazar 'Yan Ta'adda a Fadin Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi tare da kawar da ta'addanci a kasar nan
  • Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce da isassun kuɗi da kayan aiki, za a iya shawo kan matsalar 'yan bindiga cikin kankanin lokaci
  • Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kasance masu jarumtaka, da himma, tare da ci gaba da nuna ƙwarewa wajen aikin su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa 'yan ƙasa cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf domin kawar da matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron liyafa da aka gudanar a Abuja a matsayin wani bangare na bikin tunawa da ranar sojoji ta shekarar 2025.

Kara karanta wannan

2027: Rikici ya barke tsakanin gwamnan Bauchi da ministan Tinubu

Tinubu
Tinubu ya ce yana kokari domin shawo matsalar tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa Bola Tinubu ya ce gwamnati za ta ci gaba da samar da kayan aikin da suka dace da tabbatar da jin daɗin jami'an tsaro domin ganin an gama da 'yan ta'adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran Shugaba Bola Tinubu ga jami'an tsaro

Shugaban kasar, wanda Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya wakilta, ya jaddada cewa magance matsalar tsaro na bukatar haɗin kai da ƙwazon hukumomi.

“Taron tunawa da Ranar Sojoji ba kawai ana yin ta ne domin nuna godiya ga sadaukarwar jami’an tsaro ba ne,
"Har ma domin yabawa da ƙoƙarin da suka yi wajen kare ƙasa da samar da zaman lafiya,”

- Bola Tinubu

Tinubu ya kuma yi alkawarin ci gaba da kula da walwala da jin daɗin jami’an tsaro, yana mai cewa;

“Zamu tabbatar da cewa suna da kayan aiki da goyon baya domin aiwatar da aikinsu yadda ya kamata.”

Minista ya bukaci karin kudin tsaro

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi raddi ga Sanusi II kan sukar tsare tsaren Tinubu

A yayin wani taro a Abuja, Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa idan aka samar da isassun kuɗi da kayan aiki, za a iya shawo kan matsalar 'yan bindiga cikin wata biyu.

Da yake magana a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai domin kare kasafin kuɗin ma’aikatarsa na 2025, Matawalle ya bayyana rashin isassun kuɗi a matsayin babban ƙalubale.

“Kasafin kudin ma’aikatar tsaro na bana bai wadatar ba domin biyan basussuka, hakkokin ma’aikata, da kuma sauran buƙatun sojoji.
"Muna bukatar karin Naira biliyan 20 domin biyan iyalan sojojin da suka rasa rayukansu.”

- Bello Matawalle

Jan hankali kan zaman lafiya da haɗin kai

New Telegraph ta wallafa cewa shugaban kasa ya jaddada mahimmancin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’ummar ƙasa wajen magance matsalolin tsaro.

“Kalubalen tsaro da ke fuskantar mu a kullum suna bukatar jarumtaka, ƙwarewa, da sababbin hanyoyin magance su.
"Dukkan mu muna da rawar da za mu taka don tabbatar da tsaron ƙasarmu,”

- Bola Tinubu

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su zama masu fasaha da daidaita dabarun su domin tunkarar kalubalen tsaro na zamani.

Kara karanta wannan

"Allah ya albarkaci Najeriya," Hamza Al Mustapha ya taɓo batun kisan Sardauna

Yabo ga sadaukarwar sojoji

Tinubu ya yaba wa waɗanda aka karrama a taron, yana mai cewa, sadaukarwar da suka yi ta zama abin alfahari ga Najeriya.

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa za su ci gaba da yabawa kokarin sojojin wajen kare martabar ƙasa.

Haka zalika, ya bukaci sauran 'yan Najeriya su koyi darasi daga ƙwazon sojoji wajen bada gudunmawar da za ta kawo ci gaba da zaman lafiya.

Tinubu: Kokarin sulhu a Majalisar Legas

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a APC ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kokarin sasanta rikicin majalisar jihar Legas.

Legit ta ruwaito cewa shugaban majalisar da aka tsige ya ki yarda ya sauko kasa yayin da shugaban kasar ke musu sulhu a mahaifarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng