Gwamnatin Kaduna Ta Yi Nasara a kan Ta'addanci, An Shawarci Tinubu Ya Dauki Lakani
- Kungiyar BEPU ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta faɗaɗa shirin zaman lafiyar da aka fara a Kaduna zuwa jihohin Neja, Zamfara da Katsina,
- Shugaban BEPU, Dr. Isah Galadima ya bayyana cewa shirin gwamnatin Kaduna ya fara haifar da 'da mai ido wajen wanzuwar zaman lafiya
- Shirin zaman lafiya a Birnin-Gwari da gwamnatin Uba Sani ta bijiro da shi ya tattauna da shugabannin 'yan bindiga domin su zabar da makai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Kungiyar Ci Gaban Masarautar Birnin-Gwari (BEPU) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta faɗaɗa yarjejeniyar zaman lafiya da aka fara a jihar Kaduna zuwa wasu jihohin.
Kungiyar ta lissafa jihohin da za su iya amfana da saboda matsalar ‘yan bindiga da su ka hada Neja, Zamfara, Katsina, da Sakkwato a Arewacin kasar nan

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiya ta yi wannan kira biyo bayan nasarar da aka samu a shirin zaman lafiya na Birnin-Gwari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar hukumomin tarayya suka gudanar da shirin, inda manyan ‘yan ta’adda su ka zubar da makamansu.
An fara samun zaman lafiya a Kaduna
BBC Hausa ta ruwaito cewa shirin zaman lafiya a Kaduna ya tattauna da shugabannin al’umma, da manyan shugabannin ‘yan bindiga da su ka ajiye makamansu tare da rungumar zaman lafiya.
A wata sanarwa da shugaban BEPU, Dr. Isah Galadima, ya fitar a ranar Laraba, ya yaba da nasarorin da aka cimma a jihar.
Ya ce:
“Mun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta faɗaɗa wannan shiri na zaman lafiya zuwa jihohin Neja, Zamfara, Katsina, da Sakkwato, waɗanda ke fuskantar matsalolin tsaro masu tsanani.
Wannan zai taimaka wajen samar da haɗin kai na ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.”

Kara karanta wannan
ICPC ta sake cafko wani mutumin El Rufa'i, za a tafi kotu da shi kan zargin rashawa
Kungiyar Kaduna ta yaba da shirin zaman lafiya
Kungiyar BEPU ta bayyana cewa an fara samun zaman lafiya ya na dawo wa jihar sannu a hankali bayan yarjejeniyar zaman lafiya.
Sanarwar ta nuna cewa shirin zaman lafiya a Birnin-Gwari ya haifar da sakamako mai kyau, inda ya kara da cewa yanzu abin da ya rage shi ne farfado da jihar.
Dr. Galadima ya ce:
“Gyaran manyan hanyoyinmu yana da matuƙar muhimmanci wajen sauƙaƙa kasuwanci, inganta sufuri, da kuma farfaɗo da tattalin arzikin yankin.
Haka zalika, dawo da ‘yan gudun hijira muhallansu yana da muhimmanci wajen dawo da rayuwar yau da kullum.”
Gwamnan Kaduna ya samo maganin ta'addanci
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya ba da shawarwari kan yadda jihohin Arewa za su magance matsalar garkuwa da mutane da sauran matsalar tsaro a yankin.
Gwamna Uba Sani ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa da su kwaikwayi tsarin da Kaduna ta bi na yin sulhu da bangarorin da ke da hannu a rikici domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng