Lakurawa: 'Yan Ta'adda Sun Shiga Ofishin 'Yan Sanda don ba da Cin Hancin N1m

Lakurawa: 'Yan Ta'adda Sun Shiga Ofishin 'Yan Sanda don ba da Cin Hancin N1m

  • Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi ta kama mutane uku da suka yi yunkurin ba jami’anta cin hanci ga jami'inta
  • Mutanen da ake zargi sun so bayar da cin hancin domin kawo cikas ga binciken zargin ta’addanci a jihar
  • Kwamishinan ‘yan sanda ya yaba wa jami’in da ya ki karbar cin hancin tare da kira ga sauran jami'ai da su yi koyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi ta bayyana cewa ta cafke wasu mutane uku da suka yi yunkurin ba daya daga cikin jami’anta cin hanci N1.06m har cikin ofis.

Ana zargin mutanen sun cire tsoro wajen ba da cin hancin har ofishin 'yan sanda domin su hana ci gaba da binciken da ake yi kan zargin ta'addanci da ya shafi ƙungiyar Lakurawa.

Kara karanta wannan

Kayayyakin miliyoyin naira sun kone bayan tashin gobara a fitacciyar kasuwa

Yan sanda
Dan sanda ya yi watsi da cin hancin N1m Horo: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kebbi, SP Nafiu Abubakar, ya fitar ya ce babban mai binciken rundunar ya ƙi karɓar cin hancin a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An miƙa cin hanci ga ɗan sanda

Jaridar Daily Post ta ruwaito SP Nafiu Abubakar ya ce wadanda ake zargin sun hada baki don bayar da cin hancin ne a harabar sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar da ke Kebbi.

Sanarwar da ya fitar ta ce;

“Wadanda ake zargin su ne: Umaru Garba, namiji, mai shekaru 53, dan kauyen Dangandu; Alhaji Abubakar Alhaji Mamman, namiji, mai shekaru 51, dan kauyen Maimaichi, duk a karamar hukumar Arewa; da Usman Muhammadu, namiji, mai shekaru 50, dan kauyen Bakaramba a karamar hukumar Argungu.
Sun yi yunkurin bayar da cin hanci ga babban mai binciken rundunar na Naira miliyan daya da dubu sittin (N1,060,000).

Ƴan sanda sun cafke wadanda ake zargi

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mutanen gari sun yi tara tara, sun kama babban mawaƙi ɗauke da kan mace

Rundunar ‘yan sanda ta ce an cafke wadanda ake zargi da ba jami'inta cin hanci nan take a harabar hedikwatar ‘yan sanda Kebbi, kuma tuni aka fara gudanar da bincike a kansu.

Rundunar ta ce;

“Bayan kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu domin a hukunta su bisa laifin da ake zarginsu da aikatawa.”

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bello Sani, ya jinjinawa jami’an da suka yi wannan aikin bisa kwazo da jajircewarsu wajen aikinsu ba tare da cin hanci ko rashin gaskiya ba.

Ƴan sanda, sojoji sun gwabza da ƴan ta'adda

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an tsaro sun kai samame kan ’yan bindiga inda aka ceto mutum 36 daga hannun masu garkuwa da mutane a yankin Danko/Wasagu, jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun tare hanya a lokacin da mutane 36 ke dawowa daga gonakinsu a kan hanyar Mairairai/Bena, da inda su ka fara yunkurin sace su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi magana kan kisan manoma 40, ta fadi abin da ya faru

Wannan samu gagarumar nasarar ne bayan hadin gwiwa tsakanin sojoji, ’yan sanda, da ’yan banga wanda ya jawo yabo daga ɓangarori daban-daban bisa namijin kokarinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.