Zargin Ta'addanci: Tsohon Hadimin Matawalle zai Shaƙi Iskar ƴanci bayan Hukuncin Kotu
- Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci a kan kama tsohon hadimin gwamnan Zamfara, Bashir Hadejia
- Mai Shari'a Emeka Nwite ya ce ka shi ba tare da sammacin kama ba da tsare shi ba bisa ka'ida ba ya saɓa doka
- Kotun ta bayar da umarnin sakin Hadejia ba tare da wani sharadi tare da cin tarar Sufeto Janar na yan sandan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin sakin Bashir Hadejia, dan siyasa kuma dan kasuwa, wanda aka ce an kama shi bisa zargin ta'addanci. A hukuncin da mai shari’a Emeka Nwite ya yanke ranar Talata, ya ce mamaye gidansa, kamunsa ba tare da sammacin kama ba ya saba doka kuma take hakkin dan Adam nasa.
Rahoton The Cable ya ce Mai shari’ar ya ba da umarnin sakin Hadejia ba tare da sharadi ba, tare da haramta wa Sufeto Janar na ‘yan Sanda ko wakilansa sake kama shi ba bisa ka’ida ba.
Kotu ta ci tarar Sufeton ‘yan Sanda
Jaridar Peoples Gazette ta wallafa cewa kotun ta ci tarar Sufeto Janar na 'yan sanda na Naira miliyan 10 saboda ba da umarnin kama Hadejia ba tare da bin dokokin ƙasa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce an kama Hadejia ne a watan Agusta 2024 ta hannun Sashen Bincike na Sirri (FID-IRT) bisa zargin "cin amanar kasa da kokarin kifar da gwamnati.
Hadejia tsohon mai ba da shawara ta musamman ne kan ayyuka na musamman ga tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, wanda daga bisani alaƙa ta yi tsami tsakaninsu.
Tsohon hadimin Matawalle ya garzaya kotu
A takardar kara mai lamba: FHC/ABJ/CS/1235/2024 da Hadejia ya shigar ta hannun lauyansa, Mahmud Magaji, ya na tuhumar Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da Bello Matawalle.
Sauran wadanda ya shigar kara a gaban kotun sun hada da Hukumar Tsaro ta DSS, Hafsan Sojojin Ruwa, Hafsan Binciken Tsaro (DIA), da Hafsan Tsaro, inda ya nemi a sake shi.
Hadejia ya nemi kotu ta bayar da hukunci kan cewa tsare shi tun ranar 12 Agusta, 2024 ya saba wa kundin tsarin mulki tare neman diyya ta Naira miliyan 500 saboda take masa hakki.
Matawalle ya fadi hanyar magance ta'addanci
A wani labarin, kun ji cewa Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana damuwa kan ƙarancin kuɗin da ake warewa ma’aikatarsa a kasafin kuɗi don yaƙi da ta'addanci.
Matawalle da ya bayyana a gaban majalisa ya ce motocin yaƙi guda 50 kawai za su iya bai wa sojoji damar yin nasara kan ‘yan ta’adda da suka yi sansani a dazuzzukan Katsina.
Matawalle ya bayyana cewa Naira biliyan 50 da aka warewa ma’aikatar tsaro a kasafin kuɗin 2025 ya yi kaɗan, musamman idan aka kwatanta da kasafin shekarar 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng