'N11.8bn Ta Yi Kadan': Majalisa Ta Gano Matsala a Kasafin 2025 da Tinubu Ya Gabatar

'N11.8bn Ta Yi Kadan': Majalisa Ta Gano Matsala a Kasafin 2025 da Tinubu Ya Gabatar

  • Kwamitin majalisar tarayya na harkar dabbobi ya nuna damuwa kan kasafin kudin Naira biliyan 11.8 da aka warewa ma'aikatar
  • Ministan raya dabbobi, Idi Maiha ya bayyana cewa ma’aikatar tana fuskantar kalubale, ciki har da na rashin wurin aiki da kayayyaki
  • Kwamitin ya bukaci ministan da ya gabatar da karin kasafin kudi da zai fi dacewa da shirin kaddamar da aikin sabuwar ma’aikatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin hadin gwiwa na majalisar tarayya kan raya dabbobi ya nuna damuwa game da Naira biliyan 11.8 da aka ware wa sabuwar ma’aikatar raya dabbobi.

An ware Naira biliyan 10 don gudanar da manyan ayyuka da kuma Naira biliyan 1.8 don gudanar da ayyukan yau da kullum a sabuwar ma'aikatar.

Majalisar tarayya ta yi magana kan karawa ma'aikatar dabbobi kudi a kasafin 2025.
Majalisar tarayya ta ce Naira biliyan 11.8 da aka warewa ma'aikatar dabbobi sun yi kadan. Hoto: @HouseNGR, @officialABAT
Asali: Twitter

Majalisa ta tattauna kan kasafin ma'aikatar dabbobi

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro ya fadi sinadarin kawo ƙarshen ta'addanci a Najeriya

Majalisar ta nuna damuwarta kan karancin kudin da aka warewa ma'aikatar a zaman da suka yi na kare kasafin a ranar Talata, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A taron da aka yi, ministan ma'aikatar, Idi Maiha tare da manyan jami'ai da shugabannin hukumomi sun yi bayani kan kudaden da ma'aikatar ke bukata.

Idi Maiha ya bayyana cewa ma’aikatar, wadda aka cire ta daga ma’aikatar noma da tsaron abinci, ta na fuskantar manyan kalubale duk da ta fara aiki watanni uku da suka gabata.

Minista ya fadi babban aikin ma'aikatar dabbobi

Ministan ya koka kan yadda ma’aikatar ke ci gaba da zama a ofishin sakataren gwamnatin tarayya maimakon a sama mata wurin aiki na dindindin.

Ya jaddada cewa babban aikin ma’aikatar shi ne magance tasirin canjin yanayi, kirkirar damar tattalin arziki a fannin dabbobi, da kuma shigar da matasa da mata cikin harkar kiwo.

Maiha ya ci gaba da cewa za a raba manyan ayyukan hukumar a fadin yankunan siyasa na kasar da nufin jawo ra'ayin masu zuba jari na cikin gida da na waje.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kori ma'aikatan shari'a, ta ba wasu alkalan Jigawa umarnin yin murabus

Majalisa ta nemi karin kudi ga ma'aikatar dabbobi

A martaninsa, kwamitin hadin gwiwar ya bukaci ministan da ya gabatar da karin kudi a cikin kasafin na 2025 wanda zai yi daidai da bukatun kudi na ma’aikatar.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan raya dabbobi, Wale Raji, ya nuna damuwa kan goyon bayan da shugaban kasa ke ba dawa na kafuwar ma’aikatar.

Hon. Raji ya nemi karin kasafin kudi mai tsoka domin ganin cewa bukatun da ake da su na ma’aikatar sun samu shiga a shekarar 2025..

Shugaban kwamitin na majalisar dattawa, Musa Mustapha, ya kuma tabbatar da goyon bayansu wajen taimakawa ma’aikatar ta cimma manufofinta.

Gwamnan Bauchi ya kirkiro ma'aikatar kiwo

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar da shirin rigakafin dabbobi na 2025 a karamar hukumar Itas-Gadau, jihar Bauchi.

A wannan gabar ne, Sanata Bala ya sanar da kafa ma’aikatar kula da kiwon dabbobi domin magance rikice-rikicen manoma da makiyaya tare da bunkasa kiwo a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.