"Soyayya Ruwan Zuma": Saurayi Ya Bankawa Budurwarsa Wuta, Ya Ce Zai Aure Ta

"Soyayya Ruwan Zuma": Saurayi Ya Bankawa Budurwarsa Wuta, Ya Ce Zai Aure Ta

  • Jami'an ƴan sanda sun cafke wani mutumi ɗan shekara 47 a duniya, Saheed Ganiyu bisa zargin cinnawa budurwarsa wuta a Abuja
  • Mutumin ya wanke budurwar yar shekara 32 mai suna Esther da fetur, sannan ya banka mata wuta kan wani saɓani da ya shiga tsakaninsu
  • Kwamishinan ƴan sandan birnin Abuja, CP Tunji Disu ya ce za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban ƙuliya bayan kammala bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani mutum mai shekaru 47 da ke sana'ar gyaran tayoyi, Saheed Ganiyu, ya shiga hannu bisa zargin banka wa masoyiyarsa wuta a Abuja.

Wannan lamari ya faru ne a tashar motocin Jabi da ke babban birnin tarayya Abuja ranar 29 ga Disamba, 2024.

Yan sanda.
Yan sanda sun kama wani saurayi da ya cinnawa budurwarsa a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an garzaya da budurwar mai shekaru 32, Esther, zuwa babban sibitin ƙasa don ceto rayuwarta.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mutanen gari sun yi tara tara, sun kama babban mawaƙi ɗauke da kan mace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda saurayin ya ƙona sahibarsa

A cewar rahotanni, Ganiyu ya wanke Esther da man fetur sannan ya kunna wuta bayan sun samu rashin jituwa.

Yanzu haka dai matashin na tsare a ofishin ƴan sanda na Utako yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

An ce Ganiyu bazawari ne, ya taɓa yin aure amma ya rabu da matarsa, kuma yana da 'ya'ya uku.

Yan sanda sun ceci saurayin daga fushin jama'a

Kwamishinan 'yan sandan Abuja, Olatunji Disu, ya ce dakarunsa sun ceto wanda ake zargi daga fushin jama'a da suka yi yunkurin kashe shi a wajen da abin ya faru.

Kwamishinan ya bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu bayan kammala bincike.

Duk da cewa su duka aka kai asibiti bayan lamarin, Ganiyu ya samu sauki kuma ya koma hannun 'yan sanda domin fuskantar shari'a.

An ruwaito cewa masoyan biyu sun yi faɗa da juna kafin Ganiyu ya zuba man fetur a kan Esther sannan ya cinna mata wuta da maƙyasta.

Kara karanta wannan

An kama saurayin da ya yanke kan budurwarsa da wuka zai kai wa wata mata

Saurayin ya ce a shirya yake ya aure ta

A wata hira da jaridar Nigerian Tribune, Ganiyu, wanda asalin dan garin Ibadan ne a ihar Oyo, ya musanta cewa ya aikata hakan da gangan kuma ya roki izinin aurenta don gyara abin da ya faru.

Yayin da yake bayyana abin da ya faru, Ganiyu ya ce:

“A ranar Lahadi, ta ce za ta je coci, na ba ta N200 na sadaka da N2,500 na girki idan ta dawo. Amma bayan ta tafi, ba ta dawo ba har zuwa yamma.
"Na kuma yi ƙoƙarin faranta mata rai ta hanyar siyan kaya na N30,000 domin sabuwar shekara. Amma daga bisani sai na ganta a mashaya duk da cewa ta yi alkawarin ta daina.”

Ya bayyana cewa duk ƙoƙarin da ya yi na ganin ta bar wajen bai yi nasara ba, daga na ya tafi wurin aikinsa.

Wannan ya haifar da zazzafan sabani bayan ya dawo daga aiki, wanda daga bisani faɗan rikide zuwa wannan mummunan abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Cire tallafin fetur ya fara haifar da sauƙi ga talakawa, cewar hadimin Tinubu

‘Yan sanda sun tabbatar da cewa za a gurfanar da Ganiyu a gaban kotu bayan kammala bincike.

Matashi ya kashe yarinyar da zai aura a Kano

A wani labarin, kun ji cewa yan sanda sun kama wani matashi a Kano bisa zargin ya kashe budurwar da zai aura a jihar Kano.

Kotun majistare mai zama a Nomansland ta ba da umarnin a garƙame shi a gidan gyaran hali bayan an gurfanar da shi a gabanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262