Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kofar Rago, An Tura Tsageru Barzahu
- Dakarun sojoji da suke aikin samar da tsaro sun samu nasarar rage mugun iri na ƴan bindiga a jihar Zamfara a Arewa maso Yamma
- Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka wasu tantiran ƴan bindiga da suka addabi ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Tsafe
- Nasarar da dakarun sojojin suka samu ta nuna irin jajircewa da sadaukarwar da suke yi domin ganin an samu zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikici
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma sun kashe ƴan bindiga biyu a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar Askarawan Zamfara, sun kashe ƴan ta'addan da suka addabi ƙauyuka a yankin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun farmaki ƴan bindiga a Zamfara
Majiyoyin sirri sun tabbatar da cewa sojojin sun kai farmakin ne a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, 2025, a yankunan Sungawa, Yalwa da Rakyabu da ke yammacin Tsafe.
Farmakin sojojin wani ɓangare ne na yunƙurin kawar da ƴan ta'adda da suka addabi wannan yankin.
"Waɗannan ƴan ta'adda sun zama ƙarfen ƙafa wanda yake wahalar da mutanen wannan yankin."
"A koda yaushe suna fitowa su tilasta mutane biyan kuɗi da bayar da kayayyaki masu daraja. Wasu lokutan ma su kan kashe duk wanda suka ga dama."
- Wata majiya
An bayyana cewa, wannan samamen na daga cikin shirye-shiryen da dakarun sojoji suka tsara domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga al'ummar yankin.
Wannan farmakin ya kuma biyo bayan samun rahotannin sirri daga mutanen yankin da suka nuna inda ƴan ta'addan suke ɓoyewa.
Dakarun sojoji sun ƙwato makamai
Bayan kashe ƴan ta'addan biyu, dakarun sun yi nasarar ƙwace wasu makamai da suka haɗa da bindigogi da harsasai.
Hakazalika, an kuma tabbatar da cewa wasu daga cikin sauran ƴan ta'addan sun gudu da raunuka.
Ana fatan cewa wannan farmakin zai zama darasi ga sauran ƴan ta'addan da ke ɓoye a cikin dazuzzukan Zamfara, kuma zai ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Tsafe da kewaye.
Hukumomin tsaro a Najeriga suna ci gaba da ƙoƙarin ganin sun kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga.
Ƴan bindiga dai sun daɗe suna takurawa mutane a Najeriya inda suke kai hare-haren ta'addanci.
Ƴan bindiga sun sace fasinjoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun tare matafiya a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.
Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da makamai sun yi awon gaba da fasinjoji ciki har da sojoji guda uku waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna.
Ɗaya daga cikin mutanen da aka sace ya rasa ransa bayan ƴan bindigan sun harbe shi saboda ya kasa tafiya sakamakon raunin da ya samu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng