Matar Basarake Ta Rasu, Aminu Ado Ya bar Kano Kwana 4 da Hukuncin Kotu, Ya Yi Addu'a

Matar Basarake Ta Rasu, Aminu Ado Ya bar Kano Kwana 4 da Hukuncin Kotu, Ya Yi Addu'a

  • Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar ta’aziya ga Sarkin Keffi, Alh. Dr. Shehu Cindo Yamusa na Jihar Nassarawa
  • Ziyarar ta’aziyar ta biyo bayan rasuwar matar Sarkin Keffi, wacce ta kasance ginshiki a masarautar Keffi da ke Nasarawa
  • Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ya wallafa a X inda ya yi addu’ar Allah ya jikanta, ya gafarta mata
  • Wannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan kotu ta yi hukunci kan rigimar masarauta da ake ci gaba da yi a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Keffi, Nasarawa - Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alh. Aminu Ado Bayero CFR CNOL ya kai ziyara garin Keffi da ke jihar Nasarawa a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bafarawa: Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya fice daga jam'iyyar PDP, ya fadi dalili

Basaraken ya isa Keffi ne domin ziyarar ta’aziya ga Sarki, Alh. Dr. Shehu Cindo Yamusa CON bayan rasuwar matarsa a ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025.

Aminu Ado Bayero ya yi ta'azziyar rasuwar matar sarkin Keffi
Aminu Ado Bayero ya jajanta wa Sarkin Keffi,bayan rasuwar matarsa. Hoto: @HrhBayero.
Asali: Twitter

Matar Sarkin Keffi ta riga mu gidan gaskiya

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin @HrhBayero ya wallafa a shafin X a yau Talata 14 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan rasuwar marigayiyar a ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025 a jihar Nasarawa.

An gudanar da sallar jana'izar marigayiyar, Hajiya Maryam Faruq Iya a ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025.

Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III ya samu halartar jana'izar a ranar Lahadi a garin Keffi.

Sarkin Musulmi ya samu wakilcin Dan Amar din Sokoto, Alhaji Yusuf Sulaiman Yana tare da Sarkin Keffi da kuma Shehun Bama da sauransu.

Aminu Ado ya jajanta wa Sarkin Keffi

Basaraken ya kai ziyarar domin ta’aziya bayan rasuwar mai dakin Sarkin Keffi, wacce ta bar babban gibi ga masarauta da al’umma baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Ndume: Matasan Arewa sun gana da Sanatan APC don dakile kudirin haraji a majalisa

Sanarwar ta yi addu’a Allah ya jikanta, ya gafarta mata, ya kuma saka mata da aljanna firdausi.

Har ila yau, ta yi addu'ar Allah ya ba wa iyalan marigayiyar da masarautar Keffi da ma jihar baki daya hakuri.

"Mai Martaba Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero CFR CNOL JP ya isa Garin Keffi da ke Jihar Nassarawa."
"Sarkin ya je garin ne domin ta’aziya ga Mai Martaba Sarkin Keffi, Alh. Dr. Shehu Cindo Yamusa CON kan rasuwar mai dakin sa."
"Muna addu’a Allah ya jikanta, ya gafarta mata, ya kuma saka mata da aljanna firdausi."

- Cewar sanarwar

Sarki Sanusi II ya magantu bayan hukuncin kotu

A baya, kun ji cewa bayan kotu ta yi hukunci kan rigimar sarauta a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wa Allah godiya kan abin da ya faru .

Sarki Sanusi II ya bukaci al'ummar jihar Kano su cigaba da addu'ar zaman lafiya da kuma neman tsari daga masu ta da fitina.

Kara karanta wannan

'Ko a jikinmu': Gwamnan APC kan hadakar jam'iyyun adawa, ya fadi dabarbarun da za su yi

Basaraken ya yi addu'a Ubangiji ya jawo wa masu neman fitina a Kano fitintinu a rayuwarsu da kuma tashin hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.