Zargin Siyasantar da Masarauta: Gwamna Ya Sha Alwashin Kare Ta, Zai Hukunta Masu Laifi
- Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya jaddada muhimmancin masarautar Alaafin, yana mai cewa ba za a siyasantar da matsayin ba
- An zabi sabon Alaafin, Oba Akeem Abimbola Owoade, ta hanyar gaskiya da adalci ba tare da tasirin gwamna ba a cewar gwamnatin Oyo
- Makinde ya yi alƙawarin ladabtar da duk masu kokarin kawo rikici a masarautun gargajiya na jihar Oyo a sakamakon nadin
- Hakan na zuwa ne yayin da wasu daga cikin masu nadin sarauta suka soki tsarin yadda aka yi nadin da cewa ba a bi ka'ida da kyau ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ibadan, Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ya ja kunnen masu neman ta da rigima bayan nadin sabon Alaafin na Oyo.
Gwamna Makinde ya jaddada himmatuwarsa wajen kare martabar kujerar Alaafin, yana mai cewa tana da matukar muhimmanci ga al’adun Yarabawa.
Gwamna ya mika sandar sarauta ga basarake
Makinde ya bayyana hakan jiya yayin bikin ba sabon Alaafin na Oyo, Oba Akeem Abimbola Owoade sandar sarauta, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da bikin a dakin taron gidan gwamnati da ke Ibadan, inda ya nuna kudurinsa na tabbatar da gaskiya da rikon amana a masarautar gargajiya.
“Duk da matsin lamba na siyasa, ina tabbatar muku da cewa zan kare martabar kujerar Alaafin."
“Bisa mulkina, na bayyana cewa ba za a siyasantar da kujerar ba; ba za mu yi wasa da ita ba."
- Seyi Makinde
Makinde ya kara da cewa kujerar Alaafin ba tana da muhimmanci ga garin Oyo ba ne kawai, har ma ga dukkan al’ummar Yarabawa.
Gwamnan ya bayyana cewa rashin shiga harkar zaben sabon sarki da ya yi domin adalci ne, cewar Punch.
“Na gana da Oba Owoade karon farko jiya, ba tare da sanin shi ba ko wani dan takara."
- Cewar Seyi Makinde
An matsa wa gwamna kan nadin sabon sarki
Makinde ya bayyana yadda aka matsa lamba lokacin da kujerar Alaafin ta zama babu kowa a kan ta a 2022.
“Wasu sun ce sai na amince da sabon sarki, in ba haka ba, ba za a zabe ni ba, ina tabbatar muku cewa idan Oyo ba su zabe ni ba, zai fi mana yin gaskiya da adalci.".
“Za mu gurfanar da su. Idan ba su je wurin sarki ba, don neman afuwa, za mu ci gaba da shari’a da su."
- Cewar gwamnan
Yayin taya sabon sarki murna, gwamnan ya bayyana fatansa na ganin zaman lafiya da ci gaba a masarautar Oyo da al’ummar Yarabawa.
A cikin jawabinsa, Alaafin Owoade ya yi alkawarin yin aiki don cigaban garin Oyo da Najeriya, yana mai godiya ga gwamna da duk wanda ya ba da gudunmuwa a zabensa.
Masu nadin sarauta sun yi fatali da Sarki
Kun ji cewa Wasu daga cikin masu zaben sarki na Oyomesi sun ƙi amincewa da naɗin Abimbola Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo da Gwamna Seyi Makinde ya yi.
Masu nadin sarautar sun ce sun zaɓi Luqman Gbadegesin ne ba Owoade ba, suna masu cewa tsarin zaben Alaafin ya hana naɗin ta hanyar tuntuba ko son rai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng