"Mun Fahimci Abin da Ke Ciki," Malaman Musulunci Sun Goyi Bayan Tinubu kan Kudirin Haraji
- Wasu malaman addinin Musulunci sun bayyana goyon bayansu ga kudirin sauya fasalin haraji na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- A wurin wani taro da suka yi a jihar Legas, malamai da limaman Musulmi sun ce galibin masu sukar kudirin ba su fahimci abin da ke ciki ba
- A cewarsu, kudirin zai inganta rayuwar talakawa kuma zai bunƙasa tattalin arziki wanda ke kawo ci gaban ƙasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Wasu malaman addinin Musulunci da limamai sun amince da kudirorin gyaran haraji da ke gaban Majalisar Tarayya.
Malaman sun bayyana cewa kudirorin suna da kyau kuma za su rage wa talakawa wahala tare da farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar rage nauyin haraji ga ‘yan kasuwa.
Malamai sun goyi bayan kudirin haraji
The Nation ta ruwaito cewa malaman Musulunci sun goyi bayan kudirin harajin Bola Tinubu ne a wurin taron shekara da aka saba gudanarwa a jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da suka yi daban-daban, malaman sun jaddada cewa rashin fahimtar fa'idar kudirorin da kuma ƙarancin amana tsakanin al’umma ne ya jawo ce-ce-ku-ce.
Taron wanda ya gudana karo na shiɗa a Surelere an masa taken "Gyaran haraji a rayuwar Annabi Muhammad S.A.W."
'Ƴan Najeriya ba su fahimci kudurin ba'
Sheikh Ahmad Al-Bukhari Al-Mukhtar, wanda ya kafa ƙungiyar Muhammad Rosulullah Global Family, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su karanta kudirin harajin kuma su fahimce shi sosai.
Ya ce kudirin na tattare da tsare-tsare masu kyau waɗanda za su kawo ci gaba a ƙasar nan.
Sheikh Al-Mukhtar ya ce wannan taron na bayar da dama ga Musulmai su taru duk shekara domin tattauna muhimman batutuwan zamani da suka faru a rayuwar Annabi Muhammad.
Ya ce an zaɓi batun gyaran haraji ne don yi wa al’umma bayanin abin da ya ƙunsa domin su yanke shawara gwargwadon abin da suka fahimta.
Kudirin harajin Tinubu yana da amfani
Imam Shefiu Majemu, wanda ya kafa ƙungiyar Islamic Platform Society of Nigeria, ya ce waɗanda ke adawa da gyaran harajin ba su fahimci fa'idar da ke tattare da shi ba.
Ya bayyana cewa masu shirya taron sun zaɓi batun ne domin ƙara wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da mutane sun fahimci abin da gwamnati ke ƙoƙarin yi.
"Mun san gwamnati tana da niyya mai kyau, amma idan ba a fahimtar da jama’a yadda ya kamata ba, to ba za ta yi musu dadi ba. Akwai kuma batun ƙarancin amana," in ji shi.
Imam Shefiu Majemu ya yi kira ga gwamnati da ta wayar da kan al’umma domin ilmantar da ‘yan Najeriya game da waɗannan kudirorin doka na sauya fasalin haraji.
Kwamitin gyaran haraji ya gana da malamai
Kun ji cewa kwamitin shugaban ƙasa kan gyaran haraji ya gana da malamai sama da 100 kan batun kudirorin sauya fasalin haraji a Najeriya.
Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele ne ya bayyana hakan, ya ce akwao buƙatar zama da masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar nan kan batun.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng