A Karon Farko a Shekaru 10, Najeriya Ta Fara Shigo da Shinkafa daga Kasar Waje

A Karon Farko a Shekaru 10, Najeriya Ta Fara Shigo da Shinkafa daga Kasar Waje

  • Najeriya ta karbi tan 32,000 na shinkafa daga Thailand a wani matakin taimakawa wajen rage karin farashin abinci a kasar
  • Ministan Noma, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa gwamnati za ta ba da damar shigo da hatsi ba tare da biyan haraji ba na tsawon kwanaki
  • Hauhawar farashin abinci a Najeriya ya kai 41% a watan Mayu yayin da kasar ke fuskantar tsadar abinci mafi muni a cikin shekaru 30

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Najeriya ta karbi shigo da shinkafa tan 32,000, wanda shi ne na farko cikin shekaru 10, a matsayin wani mataki na rage hauhawar farashin abinci da ya addabi jama’a.

Kamfanin DUCAT da ke gudanar da ayyukan jigilar kaya ne aka ba kwangilar shigo da shinkafar daga kasar Thailand zuwa cikin kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bugi karji kan darajar Afrika a Qatar, ya fadi sirrin cigaban nahiyar

Shinkafa
An fara shigo da abinci daga kasashen ketare Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu|Ahmad Sabo
Asali: Facebook

A cewar jaridar Business Day, an kawo shinkafar ne bayan da Najeriya ta cire haraji kan hatsi kamar shinkafa, alkama, da masara a shekarar da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da wannan sassaucin haraji, an samu jinkirin fara shigo da hatsin saboda fargabar kassara manoman cikin gida wajen sayar da abin da suka noma.

Dalilin shigo da shinkafa daga kasar Thailand

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa kamfanin DUCAT, wanda ya gudanar da shigo da shinkafar Thailand zuwa Najeriya, ya bayyana dalilin hakan.

Shugaban Kamfanin DUCAT, Adrian Beciri, ya bayyana cewa;

“Najeriya tana aiki tuƙuru wajen nemo hanyoyi na fadada da ƙarfafa damar samun abinci ga ‘yan kasar.”

A cikin watanni shida da suka gabata, Najeriya ta sanar da wasu matakai da za su taimaka wajen rage hauhawar farashin abinci, wanda ya yi tashin gwauron zabo mafi tsanani a shekaru 30.

Ministan Noma da samar da wadatar abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta ɗauki matakai ciki har da ba da damar shigo da hatsi ba tare da biyan haraji ba a cikin kwanaki 180.

Kara karanta wannan

'Hanyar da Najeriya za ta kawo karshen yunwar da ta addabi al'umma gaba daya'

Gwamnati za ta fitar da tsarin sayar da abinci

Gwamnatin kasar nan ta bayyana cewa ana aiki a kan dokokin da aka gindaya a kan shigo da kayan hatsi daga kasashen waje don tabbatar da an samu abin da ake so.

Najeriya na fuskantar matsalolin hauhawar farashi da suka biyo bayan sabon shirin tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu ya fara aiwatarwa tun lokacin da ya hau kujerar Mulki.

Matakan sun hada da rage darajar Naira da kuma ƙara farashin wutar lantarki, wanda ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki, tare da hawan hauhawar farashin abinci zuwa 41%.

An fara sayar da shinkafa da sauki

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta fara sayar da buhun shinkafa a kan farashin N40,000 a wasu jihohin kasar, a wani mataki na rage radadin hauhawar farashi.

A wata sanarwa da ma'aikatar noma ta fitar, an bayyana cewa an sayar da shinkafar a kan farashin N40,000 a wasu daga jihohin kasar nan da suka hada da Legas, Ogun, da Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.