Majalisa Ta Yabi Ayyukan Sojoji a 2024, Ta Fadi Yadda Za Ta Taimaki Dakarun Najeriya

Majalisa Ta Yabi Ayyukan Sojoji a 2024, Ta Fadi Yadda Za Ta Taimaki Dakarun Najeriya

  • Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin sojoji ya tabbatar da goyon bayan su ga rundunar sojoji domin yakar ayyukan ta'addanci
  • Shugaban kwamitin, Aminu Balele, ya yaba da aiwatar da kasafin kudin sojoji na shekarar 2024, inda aka cimma fiye da kashi 99%
  • Kwamitin majalisar wakilan ya jaddada cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukan da za su tabbatar da nasarar sojojin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kwamitin majalisar wakilai kan Sojoji ya ce zai baiwa sojojin Najeriya dukkan goyon bayan da ake bukata domin magance matsalar tsaro.

Shugaban kwamitin, Aminu Balele, ya bayyana haka ne a ranar Litinin bayan ganawa da shugaban rundunar sojojin kasa (COAS), Olufemi Oluyede.

majalisa
Majalisa ta aminta da ayyukan sojojin Najeriya Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, shugaban rundunar sojojin ya bayyana a gaban ‘yan majalisar domin kare kasafin kudin sojojin Najeriya na shekarar 2025.

Kara karanta wannan

'Hanyar da Najeriya za ta kawo karshen yunwar da ta addabi al'umma gaba daya'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta jinjina yadda aka rika yaki da rashin tsaro a fadin Najeriya a shekarar 2024 da ta gabata, yayin da ake ci gaba da kai hari kan 'yan ta'adda a sabuwar shekara.

Majalisar tarayya za ta goyi bayan sojoji

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, ‘yan majalisar wakilan kasar sun jaddada goyon bayan su ga rundunar sojojin Najeriya domin a kawo karshen ayyukan rashin tsaro a Najeriya.

Shugaban kwamitin sojoji na majalisar wakilai, Balele, ya ce;

“Mu na goyon bayan sojojinmu ta fuskar tabbatar da hadin kai da aiki tare da dukkanin sauran sojojin kasar nan.”

Majalisar ta yaba da ayyukan sojoji

Aminu Balele ya ce kwamitin ya nazar i da duba yadda aka aiwatar da kasafin kudin sojojin shekarar 2024, kuma sun gamsu dada yadda aka kashe kudaden da aka ware masu.

“Abu mafi muhimmanci, kafin mu shiga cikin kasafin kudin 2025, mun tambayi tambayoyi masu muhimmanci, musamman game da abubuwan da ke faruwa a kasar da kuma hanyoyin da za a bi domin magance su.”

Kara karanta wannan

Ndume: Matasan Arewa sun gana da Sanatan APC don dakile kudirin haraji a majalisa

Ya kara da cewa sun samu muhimman bayanai a kan ayyukan sojojin, kuma akwai bukatar a kara ba su damar magance matsalolin tsaro da ya hana 'yan Najeriya bacci.

Dan majalisar ya bayyana acewa rundunar sojojin kasar nan ta aiwatar da kasafin shekarar 2024 yadda ya dace, inda ce an ya ce an 99% na abubuwan da aka sa a gaba a shekarar.

Sojoji sun fadi hanyar magance ta'addanci

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban rundunar tsaron kasar nan, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa talauci da yunwa na daga cikin abubuwan da ke ta'azzara ta'addanci.

Ya kara da cewa rashin ingantattun ababen more rayuwa da rashin ganin romon dimokuradiyya na daga cikin manyan abubuwan da ke taimakawa wajen jefa matasa a kungiyar 'yan ta'adda.

Janar Musa ya bayyana bukatar samun hadin gwiwa daga kasashen duniya da kuma daga cikin gida domin samun nasarar yaki da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu tayar da hankali a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.