Tinubu Ya Bugi Kirji kan Darajar Afrika a Qatar, Ya Fadi Sirrin Cigaban Nahiyar
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Afirka na da albarkatu da damar da za su iya kawo cigaban nahiyar
- Bola Tinubu ya gana da shugaban kasar Ruwanda, Paul Kagame, a yayin da suke halartar taro a kan muhalli a kasar UAE
- Shugaban kasar zai yi amfani da taron wajen bayyana manufofin gwamnatinsa na inganta tattalin arziki, lafiya, da sufuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Qatar - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa lokaci ya yi da nahiyar Afirka za ta mayar da hankali kan ci gabanta da dogaro da albarkatun kasa da take da su.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a yayin ganawarsa da shugaban kasar Ruwanda, Paul Kagame, a Abu Dhabi a UAE, yayin taron muhalli da ke gudana daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya jaddada bukatar Afirka ta karfafa cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cinikayya a tsakanin kasashen Afrika
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai kamata a bar Afrika a baya ba, lura da arzikin da ta ke da shi.
“Afirka na da dukkan abinda ake bukata don samun ci gaba: albarkatun kasa, mutane, da sauransu.
Lokaci ya yi da za mu mayar da hankali wajen karfafa cinikayyar cikin gida da hadin kai domin amfanar al’ummar Afirka da nahiyar baki daya.”
Shugaba Tinubu ya kara da cewa lokaci ne da ya dace da shugabannin Afirka su dauki matakan da za su bunkasa tattalin arzikin nahiyar ta hanyar yin amfani da damammakin cikin gida.
Tinubu ya yi kira ga sauran kasashen nahiyar da su hada kai wajen gina Afirka mai karfi da kuma dorewa, wanda zai zama alfahari ga duniya baki daya.
Taron Abu Dhabi a kan muhalli
Taron da ke gudana a Abu Dhabi a kan muhalli ya tattaro shugabannin kasashen duniya da masu ruwa da tsaki a fannin inganta muhalli.
Shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu domin halartar taron.
An bayyana cewa shugaban kasar Najeriya zai yi amfani da damar wajen bayyana manufofin gwamnatinsa a fannonin inganta makamashi, sufuri, kiwon lafiya, da ci gaban tattalin arziki.
Hadin kai tsakanin Tinubu da Kagame
Ganawar da Tinubu ya yi da Kagame ta kasance mai ma’ana, inda shugabannin biyu suka tattauna kan bukatar karfafa hadin kai tsakanin kasashen Afirka domin samar da ci gaba.
Tinubu ya bayyana Kagame a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda yake kokarin ganin ci gaban nahiyar.
Haka kuma, sun tattauna kan damammaki masu yawa da za su iya taimakawa wajen bunkasa kasashen Afirka ta hanyar amfani da albarkatun kasa.
Muhimmancin taron ga Najeriya da Afirka
Ana sa ran jawaban Tinubu a taron za su yi nuni da irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ke kokarin aiwatarwa a Najeriya.
Haka kuma, ana fatan zai yi amfani da taron wajen kara janyo hankalin kasashen duniya kan bukatar tallafawa Afirka domin samun ci gaba mai dorewa.
Tinubu ya yi kira ga gwamnoni
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Bola Tinubu ta yi kira ga gwamnoni kan matakin da ya kamata su dauka game da kudirin haraji.
Hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala ya ce bai dace gwamnoni su rika surutu a bainar jama'a ba kasancewar suna da damar ganawa da 'yan majalisa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng