Matsalar Lantarki na Neman Gagarar Gwamnati, Minista Ya Gaza Alkawarin Ganin Canji
- Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu ba a kai ga samo hanyar da za a kawo karshen matsalar faduwar turakun wutar lantarki ba
- Ministan Makamshi, Adebayo Adelabu ya musanta turakun wuta ya fadi sau 12 a shekarar 2024 tare da bayyana adadin ga majalisa
- Adebayo Adelabu ya ce magance matsalar faduwar wuta zai bukaci haɗin kai da hukumomin tsaro da hana lalata kayan wutar lantarki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan Makamashi, Mista Adebayo Adelabu, ta bayyana cewa ba ta samo ingantacciyar mafita ga matsalar yawan rushewar turakun wutar lantarki ba.
A shekarar 2024, matsalar wutar lantarki ta babbar barazana ga tattalin arziki, inda ta haddasa faduwar turakun wuta sau da yawa a duk faɗin ƙasar.
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Mista Adebayo Adelabu ya shaida wa Majalisar kasar nan cewa babu tabbacin cewa matsalar ba za ta ci gaba a shekarar 2025 da aka shiga ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya yi bayani cewa matsalar na iya ci gaba muddin akwai matsalolin rashin tsaro, lalata kayan wuta, da rashin ingantattun kayayyaki a bangaren.
Ministan makashi ya bayyana a gaban majalisa
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Mista Adelabu ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan makamashi domin kare kasafin kuɗin bangaren makamashi na shekarar 2025.
Ya musanta adadin da ake yayatawa cewa turakun wutar lantarki ya fadi sau 12 a shekarar 2024, yana mai cewa, sau takwas kawai aka samu wannan matsala.
Najeriya, musamman Arewacin kasar ta fuskanci matsanancin rashin wutar lantarki da ya jawo asarar tiriliyoyin Naira saboda rashin hasken wutar a shekarar 2024, wanda ya kusa jawo bore.
An shaidawa majalisa mafitar matsalar wutar lantarki
Ministan Makamashin ya bayyana cewa kawo ƙarshen matsalar faduwar turakun wuta gaba ɗaya za ta bukaci haɗin kai mai karfi, ciki har da magance matsalolin tsaro.
Ya ce;
“Babu tabbacin cewa ba za a sake samun faduwar turakun wutar lantarki ba. Abin da za mu iya yi shi ne mu tabbatar da cewa matsalar ta ragu, kuma idan ta faru, za mu gyara da gaggawa.”
Ya kuma bayyana wa kwamitin cewa ma’aikatar na aiki kafada-da-kafada da hukumomin tsaro don shawo kan matsalar, tare da dawo da tsarin aiki cikin gaggawa idan aka sake samun wani rushewar.
An kama masu lalata kayan wutar lantarki
A baya, mun ruwaito cewa kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya kama mutane shida da ake zargi da lalata manyan turakan lantarki a jihar Ribas.
njiniya Emmanuel Anyaegbulam Akpa, babban manajan TCN na yankin Fatakwal, ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
Kamfanin TCN ya kuma bayyana niyyar daukar mataki mai tsanani don tabbatar da cewa irin wannan lamarin ba zai sake faruwa ba, ya ce wadanda aka kama sun dade su na barna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng