'Hanyar da Najeriya Za Ta Kawo Karshen Yunwar da Ta Addabi Al'umma Gaba Daya'

'Hanyar da Najeriya Za Ta Kawo Karshen Yunwar da Ta Addabi Al'umma Gaba Daya'

  • Dan majalisar wakilai, ya ba da shawarar amfani da fasahohin zamani da na gargajiya don samar da wadataccen abinci da ci gaban noma
  • Gboyega Nasir Isiaka ya ce wajibi ne a inganta rarraba abinci, ajiyar amfanin gona, da tallafi ga wadanda ke cikin bukata domin rage yunwa a kasa
  • Dan Majalisar ya fadi haka yayin taron shekara-shekara na tsofaffin daliban Jami'ar FUNAAB, ya ce matsalar rashin tsaro da kawo tarnaki a noma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Abeokuta, Ogun - Dan majalisar wakilai, Gboyega Nasir Isiaka, ya yi kira da a rungumi ingantattun dabarun noma da habaka ci gaban ababen more rayuwa.

Dan Majalisar ya bukaci yin amfani da fasahar zamani tare da hikimar gargajiya wajen cimma manufar samar da abinci mai yawa da ci gaban noma a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro ya fadi sinadarin kawo ƙarshen ta'addanci a Najeriya

Dan Ya kawo hanyar yaki da yunwa a Najeriya
Dan Majalisar Tarayya, Hon. Gboyega isiaka ya kawo shawarar dakile matsalar yunwa a Najeriya. Hoto: Gboyega Nasir Isiaka.
Asali: Facebook

Dan Majalisar ya kawo shawarar yakar yunwa

Dan majalisar Yewa/Imeko-Afon na jihar Ogun, ya fadi haka lokacin da yake gabatar da lacca a taron shekara-shekara na tsofaffin daliban jami’ar noma ta Abeokuta, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Isiaka, ya yi nuni da cewa wajibi ne a inganta tsarin rarraba abinci, ajiyar amfanin gona, da kuma tallafi na musamman ga al’ummar da ke cikin matsala domin rage yunwa.

Dan siyasar da ya nemi takarar gwamna sau uku ya ce Najeriya tana fuskantar babban kalubale a harkar noma musamman wajen tsaron abinci da kariyar manoma daga hadari.

Ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar matsala, yana mai cewa manoma sun bar hekta dubu 800 na gonaki a yankin tsakiyar Najeriya saboda matsalolin tsaro.

“Nasarar harkar noma a Najeriya tana da matukar muhimmanci, duk da kasarmu tana da filayen noma masu yawa, albarkatun ruwa, da kwararrun manoma."
"Har yanzu muna fama da matsalolin rashin abinci da matsalolin tsaron manoma."

Kara karanta wannan

Abin na gida ne: Kanin tsohon gwamna ya shirya neman kujerar yayansa da ya bari

- Gboyega Nasir Isiaka

Shawarar dan Majalisar wajen inganta noma

Hon. Isiaka ya ce kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya na dogaro da noma don samun abinci, kuma yawan al’umma zai kai miliyan 400 nan da shekarar 2050.

A dalilin haka, dan Majalisar ya ce gyara bangaren noma wajibi ne don bunkasar tattalin arziki da tsaron kasa.

Ya bada shawarar kafa wuraren kiwo da za su rage rikicin manoma da makiyaya, da kuma tsara adalci a rabon filaye domin tabbatar da manoma suna da filaye masu tsaro.

Shugaban taron, Gbenga Olawepo-Hashim, ya bayyana cewa daga shekarar 2022 zuwa 2024, an rasa manoma sama da 500,000 saboda matsalolin tsaro wanda ya jawo asarar sama da Naira tiriliyan biyu.

A yankin tsakiyar Najeriya, bincike ya nuna raguwar noma da kashi 70 cikin 100, wanda ya rage yawan samun masara da doya a kasar.

Kara karanta wannan

Wani shugaban karamar hukuma ya sake nada hadimai 130 watanni 6 da nadin mutum 100

Gwamna ya fara yaki da yunwa a Jigawa

Kun ji cewa Gwamna Umar Namadi ya rattaba hannu kan yarjejeniyar noma tare da kamfanin China CAMC da Hukumar Raya Noma ta Kasa.

Yarjejeniyar za ta kawo sauye-sauye a harkar noma, tare da tallafawa manoma wajen amfani da kayan zamani a jihar Jigawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.