Wasu Yan Kano 19 da Suka Je Daurin Aure Sun Kone Kurmus, an Ceto Mutane 11

Wasu Yan Kano 19 da Suka Je Daurin Aure Sun Kone Kurmus, an Ceto Mutane 11

  • An shiga wani irin yanayi bayan afkuwar mummunan hatsarin mota da ya yi ajalin akalla mutane 19 da raunata wasu da dama a jihar Plateau
  • Mummunan hatsarin ya faru a yankin Kwana Maciji da ke karamar hukumar Pankshin a jihar Filato, mutane 19 suka rasa rayukansu, 11 kuma suka jikkata
  • Shugaban kwamitin ba da agajin gaggawa na Pankshin, John Dasar, ya tabbatar da cewa mutanen sun zo daga Kano don halartar bikin aure a Barikin Ladi
  • Motar ta kama da wuta yayin da ake ceto fasinjoji daga cikinta, lamarin ya sa mutane 19 suka kone kurmus ba tare da an iya kubuatar da su ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jos, Plateau - Wasu yan Kano da suka ziyarci jihar Plateau domin bikin daurin aure sun gamu da mummunan hatsari mota a karshen mako.

Kara karanta wannan

An kama saurayin da ya yanke kan budurwarsa da wuka zai kai wa wata mata

Mummunan hatsarin motar ya faru a karshen mako a yankin Kwana Maciji na karamar hukumar Pankshin, Jihar Filato, inda mutane 19 suka rasa rayukansu.

Mutane 19 sun kone kurmus yayin ziyarar daurin aure a Plateau
An tabbatar da mutuwar wasu yan Kano da suka je daurin aure a Plateau. Hoto: Legit.
Asali: Original

Tirela ta murkushe Keke Napep a Plateau

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa wasu mutane 11 sun jikkata a hatsarin yayin da suke dawowa daga bikin aure da suka halarta a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan wata tirela ta markade mai Keke Napep a Jos da ke jihar Filato, mutum uku sun riga mu gidan gaskiya ranar Litinin 23 ga watan Disambar 2024.

Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar hatsarin, ta ce mutum huɗu na kwance suna jinya a asibiti.

Plateau: An yi asarar rayuka a hatsarin mota

Shugaban kwamitin ba da agajin gaggawa na Pankshin, John Dasar, ya tabbatar da cewa mutanen sun fito ne daga jihar Kano don halartar bikin aure a Barkin Ladi.

Kara karanta wannan

Wani shugaban karamar hukuma ya sake nada hadimai 130 watanni 6 da nadin mutum 100

An ce bakin suna kan hanyarsu ta komawa gida ne lokacin da hatsarin motar ya faru wanda ya yi ajalin mutane da dama.

Ana tsaka da taimaka wa wadanda ke cikin motar domin ceto rayuwarsu kawai sai motar ta kama da wuta, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Yadda hatsarin mota ya ci rayukan mutane 19

“Hatsarin ya faru ne ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025 a jihar Plateau."
"Mutanen daga Kano sun zo bikin aure a Barkin Ladi, kuma suna kan hanyarsu ta komawa gida, sun bi hanyae Gindiri zuwa Bauchi wacce ta fi kusa."
"Direban da wasu mutane kaɗan sun tsira, amma mutane 19 sun kone kurmus yayin da ake kokarin ceto su daga motar da ta kama da wuta.”

- Cewar sanarwar

Shettima ya halarci auren 'ya'yan shugaban APC

A wani labarin, kun ji cewa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya halarci daurin auren 'ya'yan shugaban APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi kauyuka suna yanka mutane da wuka, sun kashe rayuka

Shettima ya samu tarba daga mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da sauran baki.

An gudanar da daurin auren a Masallacin Al-Furqan da ke birnin Kano inda Shettima ya yi addu’o’in fatan alheri da nasara ga ma’auratan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.