"Ba Sanusi II ba ne": Babban Lauya Ya Fadi Sahihin Sarkin Kano bayan Hukuncin Kotu
- M.A. Lawan ya zargi gwamnatin Kano da fassara hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ba daidai ba kan rikicin masarautun jihar
- Ya cewa har yanzu Aminu Ado Bayero ne sarki saboda hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar da ya soke hukuncin kotun jihar Kano
- Tsohon kwamishinan ya bukaci gwamnatin Kano da ta guji bayar da bayanan da za su rikitar da jama’a kan masarautu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Tsohon Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano, M.A. Lawan, ya fayyace hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rikicin masarautar Kano.
A wata sanarwa a ranar Lahadi, M.A. Lawan ya ce gwamnatin Kano ta yi wa hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara mummunan fassara ba tare da fahimta ba.
An fassara hukuncin kotu kan masarautar Kano
Jaridar Daily Trust ta rahoto babban lauyan yana cewa kotun ta yanke hukunci biyu— ɗaya ya soke hukuncin kotun tarayya, ɗayan ya soke hukuncin kotun jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta tabbatar da dokar masarautun Kano na 2024, ko ta halasta sauye-sauyen sarautar da gwamnatin Kano ta yi ba."
- M.A Lawan.
Tsohon kwamishinan ya ce hukuncin kotun ya nuna cewa kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron shari'ar masarautar amma bai goyi bayan ikirarin gwamnatin Kano ba.
"Hukuncin diyyar N10m na nan" - M.A Lawan
Tsohon Antonji Janar din ya ce:
"Soke hukuncin Mai shari'a Liman a shari’ar FHC/KN/CS/182/2024 ba shi da tasiri kan hukuncin Mai shari'a Amobeda.
"Mai shari'a Amobeda ya ba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero diyyar Naira miliyan 10 saboda tsare shi ba bisa ka’ida ba, wanda har yanzu hukuncin yana nan."
Ya kara da cewa hukuncin kotun jihar Kano da ya rushe nadin Aminu Ado Bayero a matsayin Sarki ne ya buɗe hanya ga nadin Muhammad Sanusi II.
"Nadin Sanusi II bai kammala ba" - M.A Lawan
To sai dai ya ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke wannan hukunci na kotun jihar Kano, inda ta bayar da umarnin a sake sauraron shari’ar gaban wani alkalin daban.
M.A Lawan ya ce:
"Wannan na nufin matsayin Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano yana nan, yayin da batun nadin Alhaji Muhammad Sanusi II bai kammala ba."
Ya nemi gwamnatin Kano ta daina ba jama’a bayani maras inganci game da hukuncin kotu, yana mai kira a goyi bayan masarautu.
Tsohon Antoni Janar ya gargadi gwamnatin Kano
Lawan ya jaddada cewa masarautun Kano, Bichi, Gaya, Rano, da Karaye suna bukatar goyon bayan jama’a domin ci gaban al’umma.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su cigaba da martaba al’adu da al’adun gargajiya na masarautu don zaman lafiya a jihar Kano.
Tsohon Antoni Janar ya gargadi gwamnati kan nuna rashin mutunta hukuncin kotu, yana mai jan hankali kan bin doka da oda.
Aminu Bayero zai garzaya Kotun Koli
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Aminu Babba Danagundi bai amince da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kan shari’ar sarautar Kano ba, yana cewa akwai rashin gaskiya a ciki.
Dan majalisar sarkin, ya ce zai tafi kotun koli don ƙalubalantar mayar da Muhammadu Sanusi II kan mulki, tare da nuna jajircewarsa kan goyon bayan Aminu Ado Bayero.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng