Gwamna Uba Sani Ya Samo Mafita ga Jihohin Arewa Masu Fama da Rashin Tsaro

Gwamna Uba Sani Ya Samo Mafita ga Jihohin Arewa Masu Fama da Rashin Tsaro

  • Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya samo mafita ga jihohin Arewa da suke fuskantan ƙalubalen rashin tsaro
  • Uba Sani ya shawarci jihohin da su kwaikwayi tsarin da Kaduna ta bi na yin sulhu domin samun zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikici
  • A cewar gwamnan, tsarin da ya bi na yin sulhu ya sanya an samu zaman lafiya a Birnin Gwari wanda ya daɗe yana fama da ƙalubalen ƴan bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ba da shawara ga jihohin Arewa da ke fuskantar matsalar rashin tsaro.

Gwamna Uba Sani ya shawarci jihohin da su yi koyi da tsarin da jihar Kaduna ta bi na yin sulhu domin magance matsalar rashin tsaro.

Uba Sani ya ba da shawara ga jihohin Arewa
Gwamna Uba Sani ya bukaci jihohin Arewa su yi koyi da Kaduna kan matsalar rashin tsaro Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya ce dabarar ƙin yin amfani da ƙarfin soja ta fara haifar da sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi magana kan kisan manoma 40, ta fadi abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Gwamna Uba Sani ya ba da?

Gwamnan ya bayar da wannan shawara ne a matsayin babban baƙo na musamman a wajen taron ƙungiyar mazauna Kaduna ƴan asalin jihar Zamfara.

Taron dai ya gudana ne a ɗakin taro na Arewa House, da ke Kaduna, a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairun 2025.

Gwamnan, wanda mai ba shi shawara na musamman, Malam Mohammed Jalal, ya wakilta, ya bayyana cewa tun da ya hau kujerar mulki, yake aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya a Kaduna.

Ya bayyana cewa yanzu zaman lafiya ya dawo Birnin Gwari, yankin da ya shafe shekaru da dama yana fama da rashin tsaro, kuma harkokin tattalin arziƙi sun fara bunƙasa.

Yin sulhu ya yi amfani a jihar Kaduna

Ya tunatar da cewa, ta hanyar ƙoƙarin kwamitin yin sulhu da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa tare da haɗin gwiwar hukumomin gwamnatin tarayya da jami’an tsaro, an samu zaman lafiya a Birnin Gwari.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu ya roki arziki da ya hadu da Ministan China

Idan ba a manta ba dai a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2024, Gwamna Uba Sani ya sake buɗe kasuwar Birnin Gwari, wacce ta kasance a rufe sama da shekara 10.

Haka zalika, an sake buɗe kasuwar Kidandan da ke ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, wacce aka daɗe ba a amfani da ita saboda matsalar rashin tsaro.

Gwamna Uba Sani ya yi nuni da cewa matakan yin sulhu suna taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunan da suka jima suna fama da rashin tsaro.

Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, jami’an tsaro, da al’umma wajen magance matsalolin tsaro da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan da ke fama da rikici.

Hadimar gwamnan Kaduna ta tsallake rijiya da baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari ga mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna kan harkokin siyasa, Rachael Averick.

Kara karanta wannan

"Mun gamsu da kai": Gwamna a Arewa ya samu goyon bayan takara a zaɓen 2027

Averick ta tsallake rijiya da baya a harin da ƴan bindigan suka kai mata bayan ta ƙaddamar da wani aiki a masarautar Arak da ke ƙaramar hukumar Sanga ta jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng