Bom Ya Tashi a cikin Gida Mutane na Tsaka da Barci, An Shiga Tashin Hankali

Bom Ya Tashi a cikin Gida Mutane na Tsaka da Barci, An Shiga Tashin Hankali

  • Wani abin fashewa da ake kyautata zaton bom ne ya rusa wani sabon gida da ba a jima da kammala shi ba a kauyen Umuneke da ke jihar Imo
  • Mazauna kauyen sun shiga tashin hankali da firgici bayan jin karar tashin bom din da tsakar dare, sun ce har maƙotan garin sun firgita
  • Rundunar ƴan sanda ba ta ce komai ba kan lamarin kawo yanzu, amma rahotanni sun nuna cewa ba a rasa rai ko rauni ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Wani bom da ba a san wanda ya dasa shi ba ya tarwatse da tsakar dare a kauyen Umuneke da ke yankin Mbieri a ƙaramar hukumar Mbaitoli, jihar Imo.

Rahotanni sun nuna cewa tashin bom ɗin a lokacin barci ya girgiza al'ummar da ke zaune a kauyen tare da firgita maƙotansu.

Kara karanta wannan

An kama saurayin da ya yanke kan budurwarsa da wuka zai kai wa wata mata

Taswirar jihar Imo.
Mutane sun kwana cikin firgici da wani bom ya fashe da tsakar dare a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Tashin bom ya rusa sabon gida a Imo

Jaridar Punch ta tattaro cewa bam ɗin ya fashe ne a wani sabon gida da aka kammala gininsa ba da jimawa ba kuma ya rusa gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni sakamakon wannan tashin bom wanda ya ɗaga hankalin mutane da tsakar dare.

Mutanen yankin sun shiga tashin hankali

Wani shaidar gani da ido, Iyke Njoku, ya ce:

"Ƙarar fashewar bom din ta girgiza mu sosai, mun jira ɗan lokaci, amma da ba mu ji hayaniya ko ihu ba, sai muka tafi duba abin da ya faru, muka tarar da gidan ya rushe.”
"Sai da maƙotanmu daga sauran ƙauyuka suka kira suna tambayar dalilin wannan ƙara, sannan muka fita duba abin da ya faru. Gidan bene ne, kuma masu shi sun kammala gininsa suna shirin komawa nan da watan Fabrairu.
“Abu ne mai ciwo sosai ganin duk ƙoƙarinsu ya tafi a banza saboda ba za su iya komawa gidan ba kamar yadda suka tsara.”

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya ragargaji Bola Tinubu kan hauhawar farashi

Yadda bom ya tarwatse a Imo

Wani mazaunin yankin, Mista Emma Emeka, ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa wannan ƙarar fashewa ta firgita su da daddare.

Ya ce,

“Muna cikin gida ne muka ji ƙara mai ƙarfi kamar fashewa. Da muka fito muka tarar wani sabon gidan bene ya rushe. Lamarin ya faru cikin sauri, babu wanda ya ga wanda ya aikata hakan.
“Abin da muka ji kawai shi ne ƙarar fashewar, yanzu kuma muna kallon sabon ginin ɗan’uwanmu ya zama tarkace, sun yi aiki tukuru wajen kammala ginin kuma suna shirin komawa amma yanzu ba zai yiwu ba.
“Abin mamaki, mazauna ƙauyuka na kusa sun ji wannan ƙara kuma suna mamakin inda fashewar ta fito. Dukkanmu mun kwana cikin tsoro don gudun wani hari.”

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda na jihar, DSP Henry Okoye, ya ci tura, domin lambar wayarsa ba ta shiga kwata-kwata.

Kara karanta wannan

"Har yanzu babu hujja," Rundunar soji ta yi magana kan kuskuren jefa bom a Zamfara

An kashe mutane 18 a jihar Imo

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mahara sun yi ajalin mutum 18 a kauyukan ƙaramar hukumar Orsu ta jihar Imo.

Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ta tura dakaru domin gudanar da bincike da cafke waɗanda suka aikata ɗanyen aikin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262