An Kama Saurayin da Ya Yanke Kan Budurwarsa da Wuka zai kai wa Wata Mata

An Kama Saurayin da Ya Yanke Kan Budurwarsa da Wuka zai kai wa Wata Mata

  • Mabiya wani coci sun kama wani a mutum a jihar Nasarawa mai suna Oluwatimileyin Ajayi, dauke da kan budurwarsa a cikin buhu
  • Oluwatimileyin Ajayi ya yi ikirarin cewa ya kashe budurwarsa ne saboda rashin jituwa, sannan wata mata ce ta umarce shi da ya kawo kan
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda sun tsare wanda ake zargin, kuma an gano kan ne a cikin buhun da ya wurgar a kogi kusa da cocin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Wani abu mai tayar da hankali ya faru a unguwar Orozo da ke kan iyakar Abuja da jihar Nasarawa, inda aka kama wani mutum dauke da kan budurwarsa a cikin buhu.

Lamarin ya faru ne yayin da ake gudanar da addu’o’in karshe na wani azumin kwanaki bakwai a cocin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fitar da hanyar warware rikicin kudirin haraji ga gwamnoni

Yanke kan budurwa
An kama matashin da ya yanke kan budurwarsa. Hoto: Prince Ali Hassan
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa wasu mabiya cocin sun gano wanda ake zargi bayan sun lura da wasu alamu masu ban mamaki a tattare da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama wanda ya yanke kan budurwarsa

Wakilin cocin, Caleb Umaru, ya bayyana cewa asirin Ajayi ya tonu ne a lokacin da wani daga cikin mabiya ya hango shi yana wucewa wajen kogin da ke kusa da cocin dauke da buhu.

“Wani ɗan cocinmu, Victor, ya lura da shi yayin addu’a kuma ya jawo hankalin wani ɗan uwa, Amos, domin bincike,”

- Caleb Umaru

Ajayi ya zauna a bayan cocin, amma lokacin da aka nemi ya bayyana abin da ke cikin buhun, sai ya nuna cewa babu komai.

Daga nan ne ya yi kokarin guduwa bayan wasu masu babur sun zo suna neman sa bisa zargin kisan kai.

Yadda aka gano kai a cikin buhu

Kara karanta wannan

Mazauna Benuwai sun fara tserewa daga gidajensu da 'yan bindiga suka kashe manomi

Masu babur din sun bayyana cewa suna bin Ajayi ne tun daga wani gari, inda suka lura cewa jini yana diga daga buhunsa. Wannan ya sa suka hada kai da wasu mazauna yankin domin kama shi.

Bayan an kama shi, sai Ajayi ya yi kokarin guduwa, amma aka bi shi, aka kama shi a cikin wata gona kusa da cocin. A nan ne aka tilasta shi ya dawo da buhun da ya wurgar a kogi.

Lokacin da aka bude buhun, sai aka gano cewa kan budurwarsa ne a ciki, lamarin da ya girgiza jama’a.

Meyasa Ajayi ya yanka budurwarsa?

Ajayi ya shaida cewa ya yi fada da budurwarsa ne saboda ya gano tana hira da wani mutum a waya, wanda hakan ya sa aka samu rikici tsakaninsu.

A cewar Ajayi, budurwar ta yi masa rauni da wuka, daga nan kuma ya kwace wukar ya soka mata a wuya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi kauyuka suna yanka mutane da wuka, sun kashe rayuka

Daga baya ya ce wata mata ce ta umurce shi da ya kawo mata kan budurwar, amma bai bayyana sunan matar ba.

'Yan sanda sun tafi da Ajayi

Bayan an gano abin da ke cikin buhun, faston cocin ya sanar da jama’a domin su sanar da hukumomin tsaro. Sai dai rundunar ’yan sanda ba ta iso wurin ba har sai bayan kusan rabin sa’a.

Bayan Ajayi ya samu rauni sosai saboda dukan da ya sha, an dauke shi cikin motar ’yan sanda tare da buhun da ke dauke da kan budurwar.

Boko Haram sun kashe manoma 40

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Boko Haram sun dawo da kai zafafan hare hare kan fararen hula a yankunan jihar Borno.

A wannan karon, 'yan ta'addar sun kai hari kan wasu manoma, ana zargin mayakan Boko Haram sun kashe manoma 40 da jikkata da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng