Ndume: Matasan Arewa Sun Gana da Sanatan APC don Dakile Kudirin Haraji a Majalisa

Ndume: Matasan Arewa Sun Gana da Sanatan APC don Dakile Kudirin Haraji a Majalisa

  • Kungiyar Arewa ta sake tabbatar da goyon bayanta ga Sanata Ali Ndume, wanda ke kalubalantar kudirorin canjin haraji
  • CNG ta ce tana gudanar da tarukan wayar da kan al'umma a Arewacin Najeriya, domin tuntuɓar wakilansu a kan kudirin
  • An gargadi ga 'yan majalisu da ke goyon bayan kudirin haraji da cewa za a yi watsi da duk siyasarsu saboda watsi da bukatun Arewa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kungiyar Arewa ta Coalition of Northern Groups (CNG), ta sake jaddada goyon bayanta ga Sanata Ali Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno South a Majalisar Dattawa.

Kungiyar CNG ta ce za ta ci gaba da goyon bayan matsayar dan majalisar wajen kokarin kawar da kudirin harajin Tinubu da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Arewa sun sake bijerewa kudirin haraji, sun fadi illarsa ga talaka

Senator Muhammad Ali Ndume
Matasa sun goyi bayan Sanatan Borno Hoto: Senator Muhammad Ali Ndume
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a yayin ziyarar girmamawa da aka kai wa Sanata Ndume, Shugaban kungiyar, Kwamred Jamilu Aliyu Charanchi ya ce su na tare da dan majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamred Charanchi ya bayyana cewa wannan ziyarar na da nufin musayar ra'ayoyi kan ingantattun dabaru domin dakile kudirorin haraji a matakai daban-daban.

CNG ta fara tattauna kudirin haraji

Jaridar Independent ta ruwaito Charanchi ya ce CNG na gudanar da taron tattaunawa da al'umma a fadin Arewacin Najeriya domin wayar da kan jama'a game da kudirorin harajin.

Ya kara da cewa manufar wannan aikin shine baiwa al'umma damar tuntuɓar wakilan su a majalisu da su nemi su kiyaye amana da kuma kin amincewa da canje-canjen harajin.

Charanchi ya ce:

“Za mu ci gaba da amfani da dukkan hanyoyin dimokuradiyya da ake da su domin tabbatar da cewa wadannan kudirorin, wadanda ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane, an ki su kai tsaye.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu ya roki arziki da ya hadu da Ministan China

Haraji: An shawarci shugabannin Arewacin Najeriya

CNG ta bukaci ‘yan majalisu daga Arewa da su kasance masu gaskiya ga al’ummominsu da kuma kin amincewa da kudirorin harajin, saboda rashin dacewarsu ga talakawan yankin.

A cewar kungiyar, wasu ‘yan majalisu daga Arewa sun kasa tsayawa tsayin daka, yayin da wasu kuma ke neman wani hasafi daga gwamnatin tarayya domin su goyi bayan kudirin.

Shugaban kungiyar, Kwamred Jamilu Aliyu Charanchi ya bayyana takaicin yadda wasu daga cikin jagororin yankin suke komawa ga bayan gwamnatin tarayya don amincewa da kudirin.

Kudirin haraji: CNG ta gargadi 'yan majalisu

Kungiyar matasan ta yi gargadi ga ‘yan majalisu da mambobin majalisar dokoki da suka karkata daga bukatun al’umma wajen nuna goyon bayansu ga kudirin gwamnatin tarayya.

A cewar kungiyar, za ta rika kallon 'yan majalisun dake goyon bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a matsayin masu adawa ga ci gaban al'uma, kuma za a yi watsi da siyasarsu.

Kara karanta wannan

Magana ta dawo sabuwa, kotu ta ba Ministocin Tinubu 2 umarni kan kudirin haraji

An soki gwamnatin Bauchi kan kudirin haraji

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya soki kalaman Gwamna Bala Mohammed, dangane da kudirin gyaran haraji.

Sunday Dare ya bayyana cewa irin wadannan kalamai ba su dace su fito daga gwamna ba, musamman a lokacin da ake bukatar hadin kai da tattaunawa mai ma’ana tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.