Duk da Girke Jami'an Tsaro, Rikici kan Kujerar Sakataren PDP Ya Dauki Sabon Salo

Duk da Girke Jami'an Tsaro, Rikici kan Kujerar Sakataren PDP Ya Dauki Sabon Salo

  • Tsugunne ba ta ƙare ba kan taƙaddamar da ake yi dangane da kujerar sakataren PDP na ƙasa tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye
  • Sanata Samuel Anyanwu ya koma aiki a sakatariyar PDP duk da umarnin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya sauke shi daga muƙamin
  • Sakataren na PDP ya bayyana cewa tuni ya shigar da ƙara a gaban Kotun Ƙoli kan hukuncin da ya raba shi da kujerar da yake kai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rikicin da ake kan ofishin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa ya sake ɗaukar wani salo.

Sanata Samuel Anyanwu, a ranar Litinin, ya koma ofis a matsayin sakataren PDP na ƙasa a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja

Anyanwu ya koma bakin aiki
Samuel Anyanwu a koma bakin aiki a sakatariyar PDP Hoto: Samuel Anyanwu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce komawar Sanata Anyanwu ofis ya ƙara tada ƙura kan rikicin da ake yi game da wanda ya kamata ya zama sakataren jam’iyyar PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar PDP bayan rikicin jam'iyya ya yi kamari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Anyanwu dai na taƙaddama da tsohon shugaban matasan PDP na ƙasa, Sunday Ude-Okoye, wanda ke iƙirarin shi ne sakataren jam'iyyar bisa umarnin kotu.

Ana taƙaddama kan kujerar sakataren PDP na ƙasa

A ranar Litinin, sakatariyar jam’iyyar PDP ta dawo bakin aiki bayan rufe ta don hutun bikin Kirsimeti a makon ƙarshe na watan Disamba, 2024.

Sai dai, kimanin makonni biyu da suka gabata, Ude-Okoye ya bayyana kansa a matsayin sabon sakataren jam’iyyar bisa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wacce ta sauke Anyanwu daga muƙamin.

Ude-Okoye ya ziyarci ofishin PDP tare da ganawa da wasu gwamnoni da shugabannin jam’iyyar.

A makon da ya gabata, kakakin jam’iyyar PDP na ƙasa, Hon. Debo Ologunagba, ya tabbatar da cewa Ude-Okoye ne sakataren jam’iyyar bisa hukuncin kotu.

Amma Anyanwu ya nace cewa ya shigar da ƙara a Kotun Ƙoli don dakatar da aiwatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara.

A cikin wata wasiƙa da ya rubutawa ɓangarorin jam’iyyar, Anyanwu ya jaddada cewa har yanzu shi ne sakataren PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno, sun yi barna mai yawa

PDP: Me Anyanwu ya ce bayan ya shiga ofis?

Vanguard ta ce da yake jawabi ga manema labarai bayan ya isa ofis a safiyar Litinin a sakatariyar jam’iyyar PDP, Anyanwu, ya ce ya koma bakin aiki inda ya nuna cewa Ologunagba da Ude-Okoye ba su fahimci matsayar doka ba.

Ya ƙara da cewa kakakin jam’iyyar na ƙasa kawai ya bayyana ra’ayinsa ne lokacin da ya ce shugabannin PDP sun amince da Ude-Okoye a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.

"Wannan ra’ayinsa ne ba ra’ayin jam’iyyar ba. Ya yi magana ne kawai, kuma a matsayinsa na kakakin PDP, ba zan so na caccake shi a kafafen yaɗa labarai ba. Wataƙila bai samu cikakkun bayanai ba."
"Bai san cewa an ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Koli ba. Kuma lauya ne, ya kamata ya fahimci matsayin doka."

- Sanata Samuel Anyanwu.

Jam'iyyar PDP ta cika baki kan zaɓen 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar jam'iyyar adawa a Najeriya wato PDP ta fara hango nasara kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

'PDP za ta kwace mulki a hannun APC a zaben 2027,' Sakataren jam'iyya

Sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya cika bakin cewa za su dawo kan madafun iko a 2027 bayan sun karɓe mulki a hannun APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng