Boko Haram Sun Mamaye Kauye Suna Harbi, Sun Kashe Manoma 40
- Mayakan Boko Haram sun kai farmaki a ƙauyen Kayakura da ke Doron Baga, suka kashe manoma 40 tare da jikkata da dama
- Wannan hari ya zo bayan kwana ɗaya kacal da wani hari a Chibok, inda aka kashe mutane biyu tare da ƙone wani coci
- Har yanzu ba a samu bayanin jami’an ’yan sanda kan harin ba, yayin da wasu rahotanni suka yi karin haske kan halin da aka shiga a garin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rahotanni daga Jihar Borno sun tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun kashe aƙalla manoma 40 a ƙauyen Kayakura, Doron Baga, da ke Karamar Hukumar Kukawa.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a ranar Lahadi, inda gungun maharan suka mamaye ƙauyen, suka yi harbe-harbe ba kakkautawa.
Daily Trust ta wallafa cewa harin ya faru kwanaki kaɗan bayan wani hari makamancin haka da ya yi sanadin rayuka biyu a ƙaramar hukumar Chibok.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram sun kashe manoma 40
Wani ganau ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun kutsa ƙauyen Kayakura da niyyar kashe mutane da lalata dukiyoyi.
Mutumin ya ce;
“A halin yanzu, mutane da yawa sun bace, kuma sun kashe fiye da manoma 40, yawancinsu waɗanda suka tsira daga harin Gwoza.”
Rahotanni daga wata majiya ta tsaro sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a harin ya kai 30. Wannan rashin daidaiton bayanai ya janyo damuwa a tsakanin al’ummar yankin.
Halin da aka shiga bayan harin Boko Haram
A halin yanzu, jama’a a yankin suna cikin firgici, musamman ma waɗanda suka rasa ’yan uwansu.
Wani mazaunin yankin ya ce, harin ya zo ba tare da wani gargadi ba. Maharan sun mamaye ƙauyen cikin hanzari kuma suka fara harbe-harbe.
Punch ta wallafa cewa wasu daga cikin mutanen da suka bace suna cikin tsananin fargabar kasancewa a hannun maharan Boko Haram.
Babu bayanin ’yan sanda har yanzu
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ci tura, saboda ba a iya samun sa a waya ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Duk da haka, jama’a na ci gaba da kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi, musamman a yankunan da ke fama da rikicin Boko Haram.
Matsalar tsaro da kira ga matakan gaggawa
Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke fama da matsalar tsaro mai tsanani, musamman a yankin Arewa maso Gabas.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun bayyana bukatar matakan gaggawa na kare al’umma daga hare-haren Boko Haram da sauran kungiyoyin masu tada kayar baya.
Haka zalika, al’umma na roƙon gwamnati ta kawo ƙarin tallafi ga yankin tare da tabbatar da tsaro musamman a yankunan karkara.
Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutanae
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun samu nasara a kan wasu 'yan ta'adda ciki har da masu garkuwa da mutane.
An kama masu garkuwa da mutane a jihohi daban daban ciki har da Nasarawa da Benue tare da kwato tarin makamai da suka hada da bindigogi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng