Cire Tallafin Fetur Ya Fara Haifar da Sauƙi ga Talakawa, Cewar Hadimin Tinubu
- Gwamnatin tarayya ta kara fito da dalilinta na daukar matakin cire tallafin man fetur, inda ta ce an yi haka ne don jama'ar Najeriya
- Hadimin Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci rabon tallafin kayan abinci ga 'yan jam'iyya a jihar Kano
- Abdullahi Tanko Yakasai ya kara da cewa gwamnatin Tinubu na maida hankali kan taimakawa marasa ƙarfi da masu rauni
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Hadimin Shugaban Kasa kan hulɗa da al’umma a yankin Arewa maso Yamma, Abdullahi Tanko Yakasai, ya bayyana amfanin matakan gwamnatin tarayya.
Ya tabbatar da cewa cire tallafin fetur da gwamnati ta yi ya fara samar da sauƙi ga 'yan Najeriya, kamar yadda ake gani a halin yanzu.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa hadimin ya yi wannan bayani ne yayin ƙaddamar da rabon kayan tallafin shinkafa ga mazauna ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yakasai ya ce cire tallafin fetur ya dan jawo matsaloli da fari, amma gwamnati ta ɗauki wannan mataki mai muhimmanci ne don amfanin ƙasa baki ɗaya.
Hadimin Bola Tinubu ya kare cire tallafin fetur
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Hadimin Shugaban Kasa kan hulɗa a yankin Arewa maso Yamma ya ce yanzu jama’a za su gane muhimmancin cire tallafin man fetur.
A cewar Yakasai:
“Eh, wahalhalun da ake fuskanta suna da alaƙa da cire tallafin fetur da kuma sakin darajar Naira, amma waɗannan shirye-shirye ne da Shugaban Kasa ya ɗauki matakin karfin hali saboda tun farkon wannan dimokuraɗiyya daga 1999 zuwa yau, tallafin fetur da muke bayarwa ya fi amfani ga wasu 'yan kaɗan.”
Manufar Shugaban Kasa a bayyane
Yakasai ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakin cire tallafin fetur da sauran matakai ne don samun damar adana kuɗaɗe da za a aiwatar da manyan ayyuka.
Ya bayyana cewa wasu daga ci gaba kamar gine-ginen ababen more rayuwa a fannoni kamar noma, lafiya, da sauran sassan da suka fi muhimmanci.
Ya ce:
“Tsawon shekaru matatun man fetur ɗinmu ba sa aiki, amma yanzu an fara gyaransu. Wannan yana nuna cewa tsofaffin shugabanni sun kasa gyara matatun. Ku dubi farashin man fetur, yana raguwa a hankali a kullum.”
"Gwamnatin Tinubu na son taimakon jama'a," Yakasai
Yakasai ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu wajen tallafa wa marasa ƙarfi da masu rauni a cikin al’umma, wanda ya sa aka yi rabon shinkafar tallafi ga ‘yan jam’iyya.
Yakasai ya ƙara tabbatarwa da al’umma cewa wannan rabon tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na rage wahalhalu a cikin ƙasa.
Hadimin Tinubu ya soki gwamnoni
A wani labarin, kun ji cewa Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya ce gwamnonin da ke sukar kudirin sauya fasalin haraji ba su damu da jin daɗin talakawa ba.
Daniel Bwala ya yi zargin cewa gwamnonin suna tsoron rage kuɗaɗen da ake tura masu ne, ba wai suna damuwa da rayuwar ƴan Najeriya sama da miliyan 200 ba wai kishin talaka ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng