Lauya Ya Fadi Hanyar da Ta Ragewa Aminu Ado bayan Nasarar Sanusi II a Kotu
- Wani lauya mai suna Muhammed Bello Buhari ya yi gajeren fashin baki a kan hukuncin shari’ar masarautar Kano
- Masanin dokan bai tunanin akwai hanyar da ta ragewa Aminu Ado Bayero na komawa mulki bayan an tsige shi
- Barista Muhammed Bello Buhari ya ce sai dai magoya bayan Mai martaban su jira Kwankwasiyya ta bar mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Muhammed Bello Buhari lauya ne kuma mai rajin kare hakkin Bil Adama, ya tabo hukuncin shari’ar masarautar Kano.
Bayan hukuncin kotun daukaka kara, lauyan ya fito ya na mai nuna zai yi wahala Aminu Ado Bayero ya samu yadda yake so.
Lauya ya yi sharhi kan makomar Aminu Ado
A wani tsokaci da ya yi a shafin Facebook a karshen makon nan, ya ce duk yadda aka kalla, Muhammadu Sanusi II ya yi nasara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masanin shari’ar ya kira hukuncin da nasara ga Muhammadu Sanusi II da gwamnatin Kano da ta dawo da sarkin kan karagar mulki.
Dalilinsa kuwa shi ne tun farko Mai martaba Sarki da gwamnatin Kano ne suka je kotun jihar ba Aminu Ado Bayero da aka tsige ba.
A shekarar 2024, majalisar dokokin Kano ta kawo dokar masarautar da ta tumbuke sarakunan da Abdullahi Umar Ganduje ya nada.
Wanene Sarkin Kano a idon kotu?
"Mai martaba Muhammadu Sanusi II shi ne sarkin da doka ta sani...
"domin kuwa a hukuncin kotun daukaka kara, sabuwar dokar da ta dawo da Muhammadu Sanusi II kan mulki ta na nan.
"Idan Aminu Ado Bayero yana so ya sake kalubalantar gwamnatin Kano ko mai martaba Sarki, sai dai ya tafi babban kotun jihar Kano.
"Amma kuma tsakani da Allah, har sai iya wani kai labari kuma a yanzu?"
- Muhammed Bello Buhari
Yadda Aminu Ado Bayero zai koma mulki
Lauyan ya kara da cewa yadda za a iya sauke Sanusi II kawai shi ne idan Kwankwasiyya ta rasa iko da gidan gwamnatin Kano.
Kuma ko da NNPP ta fadi zabe, MB Buhari ya ce sai an yi namijin gaske kuma an sake kirkiro wata dokar masarauta a majalisa.
Tun a shekarar bara, matashin lauyan yake cewa kundin tsarin mulkin kasa bai ba kotun tarayya hurumin shiga batun sarautar jiha ba.
A karshen rubutunsa, ya ba magoya bayan Sarki na 15 shawarar su yi hakuri da maganar sarautar gidan dabo a halin da ake ciki.
Lauyan ya saba kokarin yin sharhi irin haka da kare marasa karfi, saboda haka ne a shekarar 2021 ya kafa ‘Call A Lawyer Nigeria’.
Idan kuwa an siyasantar da lamarin, ya yi kira da cewa a tari zaben da za a yi a 2027.
Muhammadu Sanusi II ya maida martani a Kano
Ana da labari cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya magantu bayan hukuncin kotu, yake cewa masu kalubalantarsa da Allah SWT suke fada.
Hakan ya biyo bayan rigimar masarauta da ake ci gaba da yi a Kano inda aka ga mutanen Aminu Ado Bayero sun kai kara a gaban kotu.
Asali: Legit.ng