Ba a Gama Makokin Sokoto ba, Jirgi Ya Sake Jefa Bam Ya Kashe Bayin Allah a Zamfara

Ba a Gama Makokin Sokoto ba, Jirgi Ya Sake Jefa Bam Ya Kashe Bayin Allah a Zamfara

  • Ana tsoron cewa an kashe mutane masu yawa a wani kauye mai suna Kakindawa da ke jihar Zamfara
  • Babu mamaki jirgin sama ya yi kuskure ne ya saki bam, a dalilin haka aka hallaka mutane da yammacin Asabar
  • ‘Yan bindiga sun tsere ba tare da an cafke su ba, kuma a karshe jami’an tsaro suka kashe ‘yan banga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Zamfara - Mutane da dama ake samun labarin cewa sun mutu a wani a kauye da ake kira Kakindawa a karamar hukumar Muradun a Zamfara.

Bayanai sun nuna ana zargin jirgin saman jami’an tsaro ya sake jefa bam wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Jirgin sojoji
Watakila jirgin sojoji ya yi kuskuren sakin bam a kauyen Zamfara Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Zamfara: Bam ya kashe mutane a Kakindawa

Dazu da safe wani mazauni mazaunin kauyen na Kakindawa da ke jihar Zamfara, ya shaidawa jaridar Punch aukuwar wannan lamari maras dadi.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Kebbi da 'yan ta'addan Lakurawa suka kashe ma'aikata 4

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garba Umar ya ce abin ya faru ne a yammacin ranar Asabar lokacin da ‘yan banga suke yunkurin taimakawa makwabtansu a kauyen Tungar Kara.

‘Yan sa-kai sun tara dakaru bayan jin labarin shigowar ‘yan bindiga musamman da aka fahimci za su sace dabbobi kuma su yi gaba da mutane.

A maimakon jami’an tsaron su kashe ‘yan bindigan, sai kuma aka ji sun saki bam da ya yi sanadiyyar mutuwar masu kokarin taimakon jama’a.

Mutanen kauyen suna cikin takaici ganin yadda suka yi asarar ‘yan banga kuma ba a iya kama ‘yan bindigan da suka addabi al’umma ba.

'Yadda bam ya kashe mutane' - Mazaunin Zamfara

“Mu na hanyar Tungar Kara da kusan karfe 3:30 na yamma, sai wani jirgin sama kwatsam ya bayyana a wurin, ya saki bam a kan ‘yan banga.
"‘Yan bindigan sun riga sun tsere zuwa cikin jeji a lokacin."

- Garba Umar

Umar ya yi ikirarin mutane akalla 16 suka mutu da bam din ya sauka a kauyen nasu wanda kafin shi an ji cewa an yi kuskuren jefa bam a Sokoto.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bi kauyuka suna yanka mutane da wuka, sun kashe rayuka

Daga cikin wanda ya ce sun rasa rayukansu a harin har da yaron shi.

Operation Fansan Yamma za su yi bincike

Kakakin dakarun Operation Fansan Yamma da ke aiki a yankin, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya ce za su yi bincike a kan lamarin.

Da ya zanta da manema labarai a ranar Lahadin nan, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, ya ce sai sun yi bincike sannan za su yi magana a kai.

"An sake kuskuren hari a Zamfara" - Masanin tsaro

Wani masani a kan sha’anin tsaro, Sadeeq Shehu ya tabbatar da zancen a shafin Facebook.

Sadeeq Shehu wanda ya taba aiki a fadar shugaban kasa bai ba da wani karin bayani ba, illa iyaka ya ce an sake wani kuskuren a Zamfara.

Yadda bam ya 'kashe' mutane a Sokoto

Kwanaki aka ji labari cewa Darektan harkokin yada labarai na hedikwatar tsaro, ya ce ba bam ya kashe mutane a kauyukan jihar Sokoto ba

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza fada da 'yan ta'adda a jihohi, sun kwato makamai

Manjo Janar Edward Buba ya ke cewa bayan sojojin sama sun yi luguden wuta ne sai aka samu fashewar wasu abubuwa masu hadari.

Kayan yakin da ‘yan ta’adda suka boye ne ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a wani tsautsayi da ya auku a karamar hukumar Silame.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng