'Halartar Taron Kasashen Musulmi', Kiristocin Najeriya Sun Sake Taso Tinubu a Gaba

'Halartar Taron Kasashen Musulmi', Kiristocin Najeriya Sun Sake Taso Tinubu a Gaba

  • Dattawan Kiristoci sun soki Tinubu kan halartar taron Musulunci a Saudiya suna cewa hakan ya saba wa tsarin addini na Najeriya
  • Kungiyar dattawan ta yi kira ga shugabannin Najeriya da su tabbatar da bin tsarin mulki, don kauce wa raba kan addinai a ƙasar nan
  • Dattawan sun kuma caccaki Tinubu kan cire tallafin man fetur, suna cewa hakan ya kara wa 'yan Najeriya wahalhalun rayuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kungiyar dattawan Kiristoci ta Najeriya (NCEF) ta nuna damuwa kan halartar taron koli na Larabawa da kasashen Musulunci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Saudiya.

Dattawan sun bayyana cewa halartar Tinubu ya saba wa kundin tsarin Najeriya a matsayin ƙasa mai addini daban daban, ba wai Musulunci kadai ba.

Dattawan Kiristoin Najeriya sun yi magana kan halartar Tinubu taron kasashen Musulumi a Saudiya
Dattawan Kiristoci sun ga laifin Tinubu da ya halarci taron kasashen Musulunci a Saudiya. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Shugaban NCEF, Dakta Samuel Danjuma Gani, ya ce sashe na 10 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya hana gwamnati daukar bangaranci a addini, inji rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fice daga Abuja, Ya Shilla Zuwa Kasar Waje a Karo na 2 cikin Janairu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiya: Tinubu ya halarci taron Saudiya

Legit Hausa ta rahoto cewa Tinubu ya halarci taron koli na Larabawa da Musulunci na musamman da aka shirya don tattauna yanayin yankin Gabas ta Tsakiya a Saudiya.

Taron na rana ɗaya, wani bangare ne na taron Riyadh na 2023, wanda shugabannin ƙasashe da na kungiyar hadin kan Musulmi suka halarta.

Taron ya gudana ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima Mohammed bin Salman na Saudiya.

Kiristoci sun soki Tinubu kan halartar taron

Duk da haka, dattawan Kiristoci sun ce halartar Tinubu taron zai iya ƙara raba kan addinai a Najeriya.

Dakta Gani ya ce har yanzu Najeriya tana fama da matsalar bambanci na tsakanin addinai, don haka abu kalilan zai iya kawo rabuwar kawuna.

Ya ce akwai wasu yankuna da dama a Arewacin Najeriya da ake ci gaba da fuskantar take haƙƙin 'yan ƙasa na bin addininsu.

Dattawan Kirista sun gargadi gwamnatin Najeriya

Kara karanta wannan

Kafin Tinubu ya hau mulki: An ji yadda Buhari, Jonathan suka lalata tattalin arziki

Kungiyar ta NCEF ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da bin tsarin mulkin Najeriya wajen tafiyar da harkokin da suka shafi addinai.

Ta yi gargadin cewa bai kamata a samu hannun gwamnati a ayyukan da za su iya haddasa rikicin addini ba.

Dakta Gani ya kuma zargi gwamnati da gazawa wajen magance matsalolin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci a kasuwanni.

Dattawan Kirista sun soki cire tallafin fetur

Shugaban dattawan ya ce jami’an tsaro suna karɓar kuɗaɗe daga masu safarar kayan abinci, wanda ke ƙara tsadar kayayyaki a kasuwa.

NCEF ta kuma caccaki cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi, wanda ya jawo tsadar man fetur da matsalar hauhawar farashi.

Kungiyar ta ce wannan mataki ya sa 'yan Najeriya da yawa ba sa iya biyan bukatun rayuwarsu na yau da kullum.

Dattawan Kirista sun ba Tinubu shawarwari

Dattawan sun yi kira ga Tinubu ya sake duba tsarin farashin man fetur don rage wa 'yan ƙasa wahala.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu ya roki arziki da ya hadu da Ministan China

Sun kuma ce rashin kyawun manufofin gwamnati da cin hanci da kuma hare-haren 'yan ta'adda ne suka jefa ƙasar cikin matsaloli.

NCEF ta yi kira ga shugabanni da su kasance masu adalci wajen ɗaukar matakan da za su tallafi dukkan 'yan ƙasa ba tare da nuna banbanci ba.

Tinubu ya yi magana a taron kasashen Musulunci

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da bukatu da suka shafi zaman lafiya a taron ƙasashen Larabawa da Musulmi a Saudiya.

Shugaba Tinubu ya isa Riyadh, Saudiyya, domin taron kwanaki biyu, inda ake sa ran zai nemi a dakatar da yakin Isra'ila kan Falasdinawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.