'Muna kan Tsari': Abba Kabir Ya Magantu bayan Hukuncin Kotu, Ta ba Yan Kano Shawara
- Gwamnatin jihar Kano ta yi magana bayan Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan rigimar masarauta da ake yi
- Gwamnatin ta yaba wa hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya tabbatar da sahihancin matakan da aka dauka kan al’amuran masarautun jihar
- Kotun ta warware hukuncin da Kotun Tarayya ta yi a baya, tana mai tabbatar da dokokin da suka shafi nadin sarakuna da gyaran masarautun jihar
- Kwamishinan shari'a, Haruna Dederi ya bayyana cewa hukuncin ya tabbatar da adalci da bin ka’ida, tare da tabbatar da ci gaba da kare al’adun gargajiya na jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Gwamnatin Kano ta mayar da martani da Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan rigimar masarauta a jihar.
Gwamnatin ta yaba wa hukuncin da Kotun Daukaka Kara, reshen Abuja, ta yanke kan batun masarautu da ya shafi tsohon Sarkin Kano na 15, Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Antoni Janar na jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Haruna Dederi shi ya bayyana hakan a ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025, cewar Punch.
A cewarsa, hukuncin kotun ya warware matakan Kotun Tarayya ya tabbatar da cewa matakan gwamnati kan nadin sarakuna da gyaran masarautu na bisa doka.
Ya ce hakan ya tabbatar sahihancin matakan gwamnatin Kano da kuma kara musu karfin guiwa kan lamarin masarautun.
"Hukuncin Kotun Daukaka Kara ya tabbatar da sahihancin matakan gwamnati, ya kuma karfafa mana gwiwar ci gaba da kawo gyara ga tsarin gargajiya."
“Dukkan hukunci da umarni da Kotun Tarayya Kano ta bayar an soke su gaba daya ta hanyar hukuncin Kotun Daukaka Kara.”
- Haruna Dederi
Dederi ya kara da cewa hukuncin ya fayyace inda hurumin shari’a yake a kan batun nadin sarauta, yana tabbatar da dokokin kundin tsarin mulki.
Ya ce hukuncin ya nuna cewa gwamnatin jihar na aiki da ka’ida da adalci wajen yin gyare-gyare a masarautun gargajiya tare da kare al’adun jihar Kano.
Har ila yau, ya ce dokar da Majalisar Dokokin jihar Kano ta yi dangane da masarautu, da duk matakan da gwamna ya dauka, an tabbatar da su.
Saboda haka, dukkan hukumomi na gwamnati da na masu zaman kansu da jama’a an wajabta musu bin hukuncin Kotun Daukaka Kara ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na tabbatar da bin doka da adalci don ci gaba da inganta tsarin gargajiya, tare da tabbatar da wakilci da cigaban al’umma.
Asali: Legit.ng