Gwamnatin Tinubu Za Tayi Amfani da Karuwanci da Kwayoyi wajen Lissafin Tattalin Arziki

Gwamnatin Tinubu Za Tayi Amfani da Karuwanci da Kwayoyi wajen Lissafin Tattalin Arziki

  • Hukumar NBS za ta fadada yadda ake lissafin ma’aunin GDP wanda yake nuna nauyin tattalin arzikin kowace kasa
  • Wani babban jami’in NBS ya ce za a koma la’akari da ayyukan badala da alfasha domin gane hakikanin karfin tattalin
  • Domin ganin GDP ya tashi, za a lissafa da kudin da ake samu daga karuwanci, harkar kwaya zuwa inshorar lafiya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Hukumar NBS mai alhakin tattara alkaluma na kasa ta bayyana cewa za ta fito da wani sabon salon auna nauyin tattalin arziki.

Hukumar NBS za ta fara lissafi da ayyukan badala wajen lissafin ma’aunin GDP da ke bayyana karfin tattalin arzikin kasashen duniya.

Tattalin arziki
Za a canza salon auna tattalin arzikin Najeriya Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Za a canza tsarin lissafin karfin tattalin arziki

Vanguard ta rahoto cewa za a koma lissafi har da danyen ayyuka irinsu karuwanci da harkokin miyagun kwayoyi domin a auna kafin GDP.

Kara karanta wannan

"Za a haura N70,000": Gwamnatin Tinubu za ta ƙara mafi ƙarancin albashi a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ta dukufa wajen ganin an rage hauhawar farashi a kasa.

A wani taro da NBS ta shirya domin wayar da kan al’umma, hukumar ta bayyana matakan da za ta dauka domin gyara ma’aunin farashi na CPI.

Rahoton ya ce an shirya taron ne da hadin-kan NESG mai kula da harkokin tattalin arziki.

Hukumar NBS ta tarayya ta kawo shawarar a canza fasalin lissafin na GDP ne ganin wadannan ayyuka sun daidaita a ‘yan shekarun bayan nan.

A lokacin da aka yi fama da annobar cutar COVID-19, wasu ayyukan tattalin arziki sun gamu da cikas a Najeriya da sauran kasashen duniya.

GDP zai iya kara yawa a Najeriya

Idan aka fadada nauyin na GDP, za a tattaro ayyukan da suka shafi tattalin arzikin zamani, kudin ‘yan fansho da kuma harkar inshorar lafiya.

Jaridar Tribune ta ce lamarin ba zai tsaya nan ba, za a yi la’akari da asusun kudi na NSTIF da kuma kananun matatun mai da ake da su.

Kara karanta wannan

A karo na 3, gwamnatin Abba ta waiwayi 'yan fansho da Naira biliyan 5 a Kano

Wani abin da za a duba shi ne danyen ayyukan da ake yi da kuma kudin da ake biyan boyi-boyin da aka saba dauka domin aiki a gida.

Wani babban jami’in NBS, Dr. Baba Madu ya yi karin haske game da batun, yake cewa lissafi da aika-aika abu ne da aka saba a kasashe.

Dr. Baba Madu ya ce akwai kasashen da harkar kwaya ce ta ke bunkasa tattalin arziki, sai dai a Najeriya gwamnati ta haramta wannan.

Haka zalika a bangaren kasuwanci da ke kawowa mutane kudi, gwamnati za ta yi amfani da harkar domin gane nauyin karfin tattalin arziki.

Amma ya ce kalubalen da za a iya fuskanta shi ne samun alkaluma game da karuwai a Najeriya.

Alal misali akwai masu shagun da ake saida kayan yau da kullum, amma a boye su na samun ciniki da tabar wiwi ba tare da an ankara ba.

Kara karanta wannan

EFCC: Tsohon gwamna ya shiga matsala, kotu ta ƙwace masa sama da N200m

Yadda CBN ya sallami ma'aikata 1000

Labari ya zo cewa tun da aka samu canjin gwamnati ake ta fito da wasu tsare-tsaren da suka jawo ake kuka da Yemi Cardoso a bankin CBN.

Wani jami'in babban bankin na Najeriya ya shaidawa majalisar tarayya cewa babu wanda aka yi wa dole wajen ganin an ragewa ma'aikatan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng