"Za a Haura N70,000": Gwamnatin Tinubu Za Ta Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi a Najeriya

"Za a Haura N70,000": Gwamnatin Tinubu Za Ta Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu ta ce za a sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikata nan shekaru biyu
  • Ƙaramar ministar kwadago ta ƙasa, Nkeiruka Onyejeocha ce ta bayyana hakan a wani taro da ƴan kwadago a jihar Abia
  • A shekarar da ta gabata ne shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za a sake duba mafi karancin albashi na kasa nan da shekaru biyu masu zuwa.

Ƙaramar ministar kwadago da samar da ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha, ta ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi alƙawarin sake duba albashin bayan shekaru uku.

Nkeiruka Onyejeocha.
Gwamnatin Tarayya za ta sake duba mafi ƙarancin albashi na N70,000 nan da shekaru 2 Hoto: Nkeiruka Onyejeocha
Asali: Twitter

Kuma a cewarta, hakan yana nufin za a sake duba mafi ƙarancin albashi kuma a yi ƙari nan da shekaru biyu masu zuwa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yarjejeniyar $2bn: Shugaba Tinubu ya roki arziki da ya hadu da Ministan China

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onyejeocha ta yi wannan bayani ne a Umuahia, yayin wani taro da shugabannin kwadago na jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Gwamnatin Tinubu za ta yi ƙarin albashi

Ta jaddada cewa Shugaba Tinubu yana da niyya mai kyau game da batun inganta jin dadin ma'aikata kuma zai cika duk alkawuran da ya dauka.

Ministar ta ce:

"Ba za mu bar sake duba mafi karancin albashi ya dauki lokaci mai tsawo ba. A da ana yin hakan bayan kusan shekaru biyar, amma yanzu, cikin shekaru uku za a yi ƙari.
"Ma'ana nan da shekaru biyu za mu sake duba mafi ƙarancin albashi (tun da kusan shekara ɗaya kenan da amincewa da N70,000)."

A watan Yuli na shekarar 2024, Shugaba Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na Naira 70,000 tare da alkawarin sake duba shi duk bayan shekaru uku.

Onyejeocha, 'yar asalin jihar Abia, ta bayyana cewa ta yanke shawarar haduwa da ƴan kwadago, wadanda ta kira 'yan uwanta, domin taya su murnar kirsimeti da sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta amince da ƙara kuɗin kiran waya da sayen data a Najeriya

Ministar Tinubu ta gana da ƴan kwadago

Ƙaramar minista ta gana da ƴan kwadagon ne bayan ta kammala hutunta na kirismeti a gidanta da ke jihar Abia, kamar yadda PM News ta kawo.

"Ku sani kwadago wani bangare ne na gwamnati da ya kamata ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba a wurin aiki kaɗai ba, har ma da kasa baki daya.
"Ya kamata mu zauna lafiya da ku, ban da yajin aiki, inda za mu yi aiki tare da gwamnati a matsayin abokan hulda, za mu fi samun ci gaba," in ji ta.

NLC ta yabawa ministar kwadago

Shugaban kungiyar kwadago (NLC) na jihar Abia, Mista Ogbomna Okoro, ya yabawa ministar bisa nasarorin da ta samu a daga shigarta ofis zuwa yanzu.

Ya ce kungiyarsu tana alfahari da ita kuma tana fatan yin aiki tare da ita kafaɗa da kafaɗa.

Ministar, wadda ta fito daga gidan sarauta, ta kuma gana da majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Abia, inda ta yi ƙara haska masu manufofin Gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

TUC ta nemi a kara albashi a 2025

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC, Festus Osifo ya ce sun fara fafutukar a maido da ƙarin mafi karancin albashi a kowace shekara.

Osifo ya ce kamata ya yi duk shekara gwamnati ta zauna ta duba hauhawar farashin kayayyaki sannan ta ƙimanta albashin da ya dace da ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262