Kafin Tinubu Ya Hau mulki, An Ji Yadda Buhari, Jonathan Suka Lalata Tattalin Arziki

Kafin Tinubu Ya Hau mulki, An Ji Yadda Buhari, Jonathan Suka Lalata Tattalin Arziki

  • Adewole Adebayo ya ce Najeriya na fama da matsalolin tattali tun zamanin mulkin mallaka, ba wai a yanzu matsalar ta fara ba
  • Dan takarar shugaban kasar ya ce Bola Tinubu ya kara jawo tabarbarewar tattalin arziki saboda rashin kwararru a tawagarsa
  • Ya kuma yi bayanin yadda tsofaffin shugabannin Najeriya irinsu Muhammadu Buhari, Olusegun Obasanjo suka lalata tattalin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar SDP a zaben 2023, Prince Adewole Adebayo, ya zargi tsofaffin Najeriya da lalata tattalin arzikin kasar nan.

Prince Adebayo ya yi wannan zargin ne yayin wani taro da aka shirya a jihar Ondo, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu ya kara dagula matsalar tattalin ne kawai.

Prince Adewole Adebayo ya yi magana kan yadda tsofaffin shugabanni suka lalata tattalin arziki.
Dan takarar shugaban kasa ya fadi laifin Tinubu a tabarbarewar tattalin Najeriya. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Dan siyasar ya bayyana cewa Najeriya tana fama da matsaloli tun kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau kan mulki, inji rahoton This Day.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware biliyoyin Naira kan jiragen shugaban kasa a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalolin Najeriya tun kafin mulkin mallaka

Adebayo ya ce ana cika kambama batun matsalar tattalin arziki ne a gwamnatin Tinubu, amma matsalolin sun dade da faruwa tun kafin Tinubu ya zo.

Ya kara da cewa Najeriya na da matsaloli tun zamanin mulkin mallaka saboda tsarin tattalin arzikin da Turawa suka kafa domin amfanin masana'antunsu.

"A Jamhuriya ta farko, Najeriya na fuskantar matsaloli, musamman wajen aiwatar da tsare-tsaren bunkasa masana'antu da kuma kudadensu.
"A zamanin soja, Najeriya ta samu matsalolin tattalin arziki, ciki har da karancin wutar lantarki da rashin kayayyakin more rayuwa."

- Prince Adebayo.

Yadda tsofaffin shugabanni suka lalata tattali

Adebayo ya ce dole ne kowane shugaba da zai gaji Muhammadu Buhari zai fuskanci wahalhalu da fuskantar illar matsalolin da Buharin ya bari.

"Duk wanda ya karbi mulki daga hannun Buhari ya riga ya tabbata ya yi rashin sa’a domin Buhari shi kadai, ya barnatar da Naira Tiriliyan 3.7 na bashin Ways and Means.

Kara karanta wannan

Kudirin haraji: Malamin musulunci ya ba Arewa shawarar gujewa zaman gori

“Goodluck Jonathan ya kusa gamawa da tattalin arzikin Najeriya kafin Buhari ya zo, al’amura ne da suka shafi gadon matsala.
“Obasanjo ya sauka ya bar kudi masu tsoka a baitul mali, amma ya barnatar da kudi a cikin shekaru takwas da ya yi ba tare da gina ababen more rayuwa ba.
“Ya sauka ba tare da kammala ayyuka ba, kamar titin Kudu zuwa Yamma, gadar Neja, titin Kaduna- Kano, layin dogo, wutar lantarki da sauransu."

- A cewar dan takarar shugaban kasar na SDP.

Tabarbarewar tattalin arziki a hannun Tinubu

Dan takarar shugaban kasar, ya yi ikirarin cewa ba za a iya cewa Tinubu ya samu 'yan Najeriya a cikin aljanna ba, ko kuma a ce Tinubu ne ya shigar da su cikin wuta ba.

Dangane da irin gudunmawar Tinubu wajen kara tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya, Adebayo ya bayyana cewa shugaban ya kara dagula lamura ne kawai.

Kara karanta wannan

"An shiga wahala bayan zaben Tinubu," Sanatan APC ya fadi manufar gwamnati

Ya ce:

"Matsalar Tinubu ita ce kokarin warware matsalar mutum mai ciwon kai ta hanyar kara masa azabar ciwon, maimakon ba shi maganin rage radadin ciwo."

Ya kara da cewa Tinubu ya kara tabarbarewar tattalin arziki saboda rashin fahimtar ilimin tattalin arziki ko kuma yin aiki da wadanda suka kware.

Laifin Tinubu a lalacewar tattalin arziki

Adebayo ya ce Tinubu ya tarar da tattalin arziki a cikin matsala, amma ya kara dagula al'amuran ne saboda rashin iya tafiyar da tattalin.

Ya ce Tinubu yana gane harkokin kudi, amma bai fahimci tasirin tattalin arziki kan matsalolin al’umma gaba daya ba.

Ya kuma nuna cewa Wale Edun, wanda ke cikin gwamnati, kwararre ne a harkokin banki, amma ba masanin tattalin arziki ba ne.

A cewar Adebayo, Wale Edun zai iya tafiyar da kudi a matsayin mai zuba jari, amma bai san tasirin wadannan kudi ga tattalin arziki ba.

Obasanjo ya hana Gaddafi shigo da makamai

Kara karanta wannan

'Ku dage da addu'a;" Malamin addini ya hango abin da zai faru da Najeriya a 2025

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Olusegun Obasanjo ta sha dakile shirin tsohon shugaban kasar Libiya, Muammar Gaddafi na shigo da makamai Najeriya.

Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya yi bayanin yadda aka hana Gaddafi shigo da makamai a shekarar 2000 da kuma 2006.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.