Borno: 'Yan Boko Haram Sun Kai Mummunan Hari Ofishin 'Yan Sanda, an Rasa Rayuka

Borno: 'Yan Boko Haram Sun Kai Mummunan Hari Ofishin 'Yan Sanda, an Rasa Rayuka

  • Rahotanni sun ce 'yan Boko Haram sun kai hari a Gajiram, Nganzai, inda suka kashe ‘yan sanda biyu kuma suka raunata wani
  • Rundunar hadin gwiwar fararen hula da ‘yan sanda sun dakile harin tare da gano gurnetin hannu guda biyu da ya halaka jami'an
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi Allah wadai da wannan mummunan hari da mayakan Boko Haram suka kai kan ofishinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - 'Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari kan ofishin ‘yan sanda a Gajiram, karamar hukumar Nganzai ta jihar Borno.

An ce mayakan sun halaka jami'an 'yan sanda biyu a yayin wannan farmaki.

Rundunar 'yan sanda ta rasa jami'anta yayin da Boko Haram ta farmaki ofishinta na Borno
Boko Haram ta kashe wasu jami'ai biyu yayin da ta farmaki ofishin 'yan sanda na Borno. Horo: @Princemoye1
Asali: Twitter

Boko Haram ta kai hari ofishin 'yan sanda

Rahoton Channels TV ya ce wani jami’i ya samu mummunan rauni yayin musayar wuta tsakanin ‘yan ta’addan da ‘yan sanda da ke bakin aiki.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza fada da 'yan ta'adda a jihohi, sun kwato makamai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan dauki ba dadi ne aka kori 'yan ta’addan da taimakon rundunar hadin gwiwa ta fararen hula da ke da sansani a kusa da ofishin 'yan sandan.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa 'yan Boko Haram din sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Laraba.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da harin

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa babu wani muhimmin gini ko kayan tsaro da aka lalata yayin harin.

Sai dai kuma wata sanarwar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:10 na safiyar Alhamis.

ASP Kenneth Daso, kakakin rundunar ‘yan sandan Borno, ya ce an gano gurnetin hannu guda biyu yayin duba ofishin da aka farmaka.

Abin da sanarwar 'yan sanda ta ce

Sanarwar ASP Kenneth ta ce:

“Da misalin karfe 12:10 na safiyar ranar 9 ga watan Janairun 2025, wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Nganzai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'addanci ga boka, sun kashe masa 'ya'ya 3

“Jajurtattun jami'an da ke aiki sun sun fatattaki ‘yan ta’addan bayan musayar wuta, amma ‘yan ta’addan sun jefa gurnetin hannu wanda ya fada kan wani tantanin 'yan sanda.
"Sakamakon jefa gurnetin, wasu jami'an 'yan sanda biyu sun samu munanan raunuka da ya kai ga ajalinsu."

Kwamishina 'yan sanda ya jinjinawa jami'ai

Sanarwar ta ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Yusufu Lawal ya jagoranci jami'ai wajen duba ofishin da aka kai wa farmakin, inda aka gano gurtenin da ya halaka jami’an biyu.

Jami'an bincike da lalata abubuwan fashewa EOD–CBRN sashi na 13 na Maiduguri sun gano gurnetin hannu guda biyu yayin duba ofishin da aka farmaka.

An kai gawar wadanda suka mutu zuwa babban asibitin Maiduguri don gudanar da bincike.

CP Yusufu Lawal ya yaba da jaruman jami’an da suka dakile harin kuma ya yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Garuruwan Borno 2 na hannun Boko Haram

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Borno, 'yan ta'adda sun kashe sojojin Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa kakakin majalisar Borno ya bukaci gwamnatin tarayya ta kafa birgediyar soja a Guzamala da Kukawa domin dawo da tsaro a yankin.

Rt. Hon. Abdulkarim Lawal ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum kan kokarin ci gaba duk da matsalar Boko Haram da ke addabar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.