Dattawan Arewa Sun Yi Martani ga Kwankwaso a kan Fitar da Ɗan Takara
Kalaman tsohon gwamnan Kano, kuma tsohon Sanata, Rabi'u Musa Kwankwaso a kan dattawan Arewa bai yi wa wasu daga cikin manyan shiyyar daɗi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana rashin jin daɗin abin da ya kira 'katsalandan' a harkokin fitar da ɗan takara.
Madugun Kwankwasiyya ya fadi kalaman a kan dattawan yankin, inda ya ke ganin abin da ya fi dace wa da dattawan shiyyar, shi ne su bar maganar fitar da ƴan takara a hannun jam'iyyun siyasa.
Legit ta tattauna da kungiyar ACF, wacce ta ƙunshi dattawan Arewa masu ra'ayoyin siyasa daban-daban, inda ta bayyana matasayarta a kan fitar da ɗan takara a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sukar Kwankwaso kan dattawan Arewa
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kira dattawan Arewa da 'tsirarun mutane.'
Ya ce su kan yi katsalandan wajen shiga lamarin da bai shafe su ba, watau tsayar da ɗan takarar shugabancin Najeriya da zai wakilci jama'a a kakar babban zaɓe.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce;
Wannan abu da suke yi na zalunci yana haifar da tarnaki a tsakanin al’umma."
"Bai kamata dattawanmu su riƙa nuna son rai wajen zaɓen ‘yan takara ba."
Martanin dattawan Arewa kan tsaida 'yan takara
A tattaunawarsa da Legit, jami'in hulda da jama'a na ƙungiyar ACF reshen jihar Kano, Bello Sani Galadanci ya bayyana cewa babu ruwan dattawan Arewa da fitar da ɗan takara.
Ya ce duk da ƙungiyar ta haɗa dattawa masu ra'ayin siyasa daban-daban, amma a ƙungiyance, ACF ba ta da ra'ayin siyasa da ta ke amfani da ko goyon bayan ɗan takara.
Bello Sani Galadanci ya ce;
"ACF ƙungiyar kare muradu, martaba da mutuncin al'ummar jihar Arewa ce."
"Idan ma ce jihar Arewa, ta haɗa jihohinmu 19 na Arewa, manufarta shi ne a samu zaman lafiya tsakanin Arewa da sauran ɓangarorin ƙasar nan a abin da ake kira tarayyar Najeriya.
Ya tabbatar da cewa babu ruwan dattawan Arewa da siyasa, illa fafutukar ilimantar da jama'a wajen zaɓen mutum na gari.
"Dattawa ba su da kataɓus," Masani
Farfesa Kamilu Sani Fagge, masani ne a kan harkokin siyasa a jami'ar Bayero ne a Kano, ya shaida wa Legit cewa dattawa yankin ba su da ta cewa a wajen fitar da ɗan takara.
Farfesa Fagge ya kara da cewa gwamnoni ne su ka fi kowane 'yan siyasa tabuka wani abu a wajen tabbatar da tasirin dan takarar shugaban kasa a Najeriya.
Dattawan Arewa sun soki gwamnatin Tinubu
A baya, kun ji cewa kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bayyana rashin jin daɗinta kan sabuwar dokar haraji da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gabatar.
A cewar NEF, dokar za ta iya kawo rabuwar kai a ƙasar, musamman a Arewacin Najeriya, inda aka bayyana damuwa kan rashin shigar da masu ruwa da tsaki a shirya ta.
Asali: Legit.ng