A Karo na 3, Gwamnatin Abba Ta Waiwayi 'Yan Fansho da Naira Biliyan 5 a Kano
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce za ta fara biyan kudi a mataki na uku domin sauke nauyin tsofaffin ma'aikatan Kano
- Gwamnati ta ce an biya bashin fansho na Naira biliyan 11 daga cikin Naira biliyan 43 da ma'aikatan da suka dade su na hidima
- Gwamnatin ta jaddada jajircewarta wajen ganin an biya dukkan basussukan fansho da ake bin tsofaffin ma’aikata sun samu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai kaddamar da mataki na uku na biyan hakkokin 'yan fansho a ranar Alhamis.
Ana sa ran biyan na wannan lokaci zai kai kimanin Naira biliyan biyar, wanda aka tsara don rage radadin wahala ga tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya.
Wannan a ƙunshe a cikin sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Darakta Janar na yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta bayyana cewa za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a Fadar Gwamnati da ke Kano domin fara biyan kudaden karo na uku tun bayan hawan NNPP mulkin Kano.
'Mun damu da 'yan fansho," Gwamnatin Abba
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin Kano ta jadadda cewa ta jajirce wajen ganin an inganta rayuwar 'yan fansho da suka sadaukar da shekaru masu yawa wajen hidimtawa jihar.
Sanarwar ta ce tun bayan hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf, gwamnatin ta dauki biyan fansho a matsayin muhimmin abu, inda aka sanya tsari mai inganci domin kula da tsarin.
Yadda gwamnatin Kano ta fara biyan fansho
Sanarwar ta bayyana cewa a mataki na farko, gwamnatin ta ware Naira biliyan 6 domin biyan tsofaffin ma’aikatan da ke kasa da matakin aiki na 10.
A mataki na biyu kuma, gwamnatin ta sake sakin Naira biliyan 5 domin raba wa tsoffin ma’aikata da suka yi aiki tsawon shekaru 35.
Sanarwar ta ce;
"Tun daga lokacin da aka hau mulki, wannan gwamnati ta biya sama da Naira biliyan 11 daga cikin bashin Naira biliyan 43 da ake bin jihar a matsayin fansho. Wannan abu ne da aka yi cikin matakai biyu domin rage radadin wahalar 'yan fansho.”
Gwamnatin Kano za ta cika alƙawura
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sake nanata aniyarta na ganin an biya dukkan basussukan fansho da aka gada, tare da tabbatar wa 'yan fansho a gwamnatin baya
Haka kuma an ba su tabbacin za su samu hakkokinsu a kan lokaci, a wani matakin cika alkawuran kamfen na gwamnatinsa ta dauka wajen kyautata jin dadin al’umma.
Gwamnan Kano ya taimaki 'yan fansho
A baya, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ƙaddamar da shirin biyan kuɗaɗen giratuti kashi na biyu a jihar a ranar Asabar, 29 Yuni, 2024.
A yayin ƙaddamar da wannan shiri a gidan gwamnatin jihar, Gwamna Abba ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatin baya ta lalata tsarin fansho a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng