Gwamna Ya Gama Sukar Tinubu, Zai Kashe N400m don Sayen Kwamfuta 6
- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ware Naira miliyan 400 domin sayen kwamfutoci guda shida ga ofishin SSG
- Gwamnatin jihar Bauchi ta ware Naira miliyan 170 don sayen janareta da zai rika samar da hasken wuta ga sakataren na gwamnati
- Shugaban kungiyar CAJA, Kwamred Kabiru Sa’idu Dakata, ya yi zargin cewa aringizon kuɗin talakawa ne da ba zai amfane su ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi - Wani bangare na kasafin kudin 2025 da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya gabatar a gaban majalisa ya fara daukar hankali.
An gano yadda gwamnan, wanda ya yi ƙaurin suna a wajen sukar manufofin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai kashe wasu miliyoyin Naira a kan sayo kwamfuta.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Naira miliyan 400 aka ware a cikin kasafin kuɗin 2025 domin sayen kwamfutoci guda shida a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bauchi za ta sayi janaretar N170m
Gwamnatin jihar Bauchi ta tanadi kudi da ya kai Naira biliyan 1 don "sayen fili domin gina ofisoshi da gine-gine, daga cikin kasafin kudin 2025.
Haka kuma ta ce za ta kashe akalla Naira miliyan 170 domin sayen janareta da zai samar da wutar lantarki ga ofishin SSG.
An soki aringizo kudin gwamnatin Bauchi
A zantawarsa da Legit, Kwamred Kabiru Sa’idu Dakata, shugaban kungiyar CAJA mai fafutukar tabbatar da adalci da daidaito a Najeriya (CAJA) ya ce wannan aringizo babban kalubale ne.
Ya ce sau da dama, hukumomi su na amfani da dabarun kasafta makudan kuɗi a kan wasu abubuwa domin samun damar wawashe dukiyar talakawansu.
Kwamred Dakata ya ce irin wadannan ayyuka ba su ne abin da jama'a ke bukata a wannan lokaci da ake fama da matsin rayuwa da hauhawar farashi ba.
"A kan fake da gwamnati a wasu lokuta," CAJA
Kwamred Kabiru Dakata ya bayyana cewa kudin da aka ware domin sayen kwamfutoci a jihar Bauchi daidai ya ke da cin amanar talakawa.
""Kwamfuta guda shida a kan N400m, yanzu mu ɗauke shi kan shi abin da ya shafi kwamfuta, idan ita za a saya, da N400m, guda nawa za a saya da za a yi aiki da ita, ko dai a ofisoshin gwamnati ko a taimakawa dalibai, ko kuma matasa da za su iya amfani da irin wadannan kwamfutoci domin yin ayyukanmu?"
Ya ce wannan kalubale ne ga al'umma na tabbatar da taje abubuwan da ake sa wa a ciki kasafin kudi domin jawo hankalin gwamnoni, domin wasu lokutan ba su da masaniya.
Gwamnatin Bauchi ta soki Bola Tinubu
A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Bauchi ta ce wasu gwamnoni ba sa shiri da shugaban kasa Bola Tinubu, sakamakon wasu kudurorin da suka ce ba su taimaka wa jama'a.
Ya yi zargin cewa shugaban kasar ba ya karbar shawarwari, wanda hakan ke jefa al'umma cikin wahala, musamman ta hanyar bijiro da ƙudirin gyaran haraji da sauran matakan gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng