Tinubu Ya Yi Alhinin Kisan Sojoji a Borno, Ya ba da Umarni
- Shugaban ƙasan Najeriya ya nuna alhininsa kan kisan da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi wa dakarun sojoji a jihar Borno
- Mai girma Bola Tinubu ya yi ta'aziyya ga rundunar sojojin kan wannan babban rashin da aka yi na jami'an tsaro
- Ya yabawa sojojin kan martanin da suka kai bayan harin, inda suka samu nasarar hallaka ƴan ta'adda masu yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya nuna alhininsa kan kisan da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi wa sojoji a jihar Borno.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kashe sojojin ne a wani hari da suka kai a sansaninsu da ke Sabon Gida a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar kisan sojoji
Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyyar rasa sojojin ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya aika da saƙon ta'aziyyarsa ga hukumomin sojoji kan harin ƴan ta'addan wanda ya yi sanadiyyar rasuwar jami'an tsaro shida, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Jiragen yaƙin da aka turo daga birnin Maiduguri, sun kai farmaki kan ƴan ta'addan da suka kai harin yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Wane umarni shugaba Tinubu ya ba da?
Ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin lamarin, tare da ɗaukar darasi domin kaucewa faruwar irin hakan a nan gaba.
"Jarumtakar da rundunar sojoji ta nuna a wannan lamarin, ta tabbatar da ƙarfinsu da shirinsu na fuskantar duk wata barazana ga tsaron kasa."
"Hakan ya zama shaida kan jajircewarsu wajen kawar da ta’addanci, domin samar da makoma mai inganci ga dukkanin ƴan Najeriya."
"Ina miƙa godiya ta musamman tare da ta’aziyya ga rundunar sojoji da jami’an tsaro a madadin ƙasarmu."
"Sadaukarwarku da jajircewarku ba za ta tafi a banza ba, kuma muna tare da ku a wannan yaƙin da ake yi na kawar da duk wata barazana."
- Bola Tinubu
Tinubu ya jinjinawa dakarun sojoji
Shugaba Tinubu ya jinjinawa rundunar sojojin bisa martanin da suka mayar wajen farmakar ƴan ta'addan da suka kawo harin.
Tinubu ya bayyana cewa harin sama da aka kai ya yi sanadiyyar hallaka ƴan ta’adda da dama da kuma lalata kayayyakin aikinsu yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Shugaban ƙasan ya buƙaci rundunar sojoji da su ɗauki matakan yaƙi da ƴan bindiga da ƴan ta’adda ta hanyar kai farmaki a sansanoninsu.
Tinubu ya yi kira ga ƴan Najeriya da kafafen yada labarai da su goyi bayan kokarin rundunar sojoji wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a ƙasa baki ɗaya.
An buƙaci Tinubu ya kafa sansani a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Borno, ya buƙaci gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu, ta samar da sansanon birgediyar soja a wasu ƙananan hukumomi biyu na jihar.
Rt. Hon. Abdulkarim Lawan ya buƙaci a samar da sansanonin ne a ƙananan hukumomin Guzamala da Kukawa domin ƙwato su daga hannun ƴan ta'addan Boko Haram.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng