Zambar $4.5bn: Kotu Ta Yi Fatali da Buƙatar Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele
- Kotu ta soke bukatar Godwin Emefiele da ke tuhumar huruminta na sauraron zargin da hukumar EFCC ta ke yi masa
- Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati na zargin Mista Emefiele da badakalar Dala Biliyan 4.5 da N2.8bn
- Mai shari’a, Rahman Oshodi ya soke wasu daga cikin zarge-zarge 26 da EFCC ta gabatar, amma shari’ar Emefiele za ta ci gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kotun laifuka na musamman ta Jihar Legas, ta soke bukatar da tsohon gwamnan Bankin CBN, Godwin Emefiele, ya shigar, gabanga.
Mista Godwin Emefiele ta bakin lauyansa, Olalekan Ojo (SAN), ya kalubalanci ikon da hurumin kotun wajen sauraron kara da Hukumar EFCC ta shigar a kansa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa EFCC na tuhumar Emefiele kan zargin zamba na Dala biliyan 4.5 da Naira biliyan 2.8 a lokacin ya na jagorancin Babban Bankin Kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC: Godwin Emefiele ya kalubalanci kotu
A ranar da aka yi zaman sauraron shari’a na karshe a ranar 12 ga Disamba, 2024, lauya na Emefiele, Olalekan Ojo (SAN), ya ce kotun ba ta da ikon sauraron shari’ar a Legas.
Ojo SAN ya bayyana cewa laifuffukan da ake tuhuma, ciki har da cin hanci da amfani da mukami ba su cikin ikon kotun ta musamman ta Legas. Bayan wadannan hujjoji, Mai Shari’a Oshodi ya dage shari'ar zuwa 7 ga Janairu, 2025, don yanke hukunci kan bukatar da aka shigar game da ikon kotun.
Kotu ta yi hukunci a kan koken Emefiele
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa a ranar Laraba, 8 Janairu, 2924 ne kotun sauraron shari'ar laifuffuka na musamman ta bayyana matsayin shari'ar Emefiele da ke gabanta.
Mai Shari’a Rahman Oshodi, a cikin hukuncinsa, ya bayyana cewa kotun na da ikon sauraron shari’ar Emefiele da kuma wanda ake tuhuma tare da shi, Henry Omoile.
Emefiele: Kotu ta soke wasu bukatun EFCC
Mai Shari’a Oshodi ya soke wasu daga cikin tuhume-tuhume guda hudu daga cikin guda 26 da EFCC ta shigar a kan wanda ake tuhuma, Mr. Godwin Emefiele.
Mai Shari’a Oshodi ya ce kotu ba ta da hurumin zarge-zargen da aka soke ya kara da cewa:
"Rarraba kudaden musayar kasashen waje ba tare da wani dalili ba ba a bayyana shi a matsayin laifi ba a cikin kowanne doka da aka rubuta. Saboda haka, bukatar canza ƙididdiga daga ɗaya zuwa hudu ta samu nasara kuma an soke su."
EFCC: Kotu ta dage sauraron shari’ar Emefiele
EFCC ta gurfanar da Emefiele a gaban kotu kan zarge-zarge guda 26, wanda suka shafi cin hanci da kuma rarraba Dala biliyan 4.5 da Naira biliyan 2.8 ba bisa ka’ida ba. Sai dai, hukuncin bai samu a ranar da aka saba ba, wanda ya sa aka dage zuwa ranar Laraba, 8 ga Janairu, 2025, daga nan, an sake ɗage ta zuwa 24 da 26 ga Fabrairu, 2025.
Tsohon gwamnan bankin CBN ya nemi beli
A wani labarin, kun ji cewa hukumar Yaki Da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan Bankin CBN, Godwin Emefiele, a gaban kotu.
Ana zarginsa laifuffukan da suka shafi canjin kudi, abin da Emefiele ya ki amincewa da laifuffukan da ake zarginsa da su, kuma lauyansa ya roki kotun ta bayar da belinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng