'Yan Sanda Sun Gwabza Fada da 'Yan Ta'adda a Jihohi, Sun Kwato Makamai
- Rahotanni na nuni da cewa ’yan sanda sun kara kaimi da dabaru wajen magance matsalar garkuwa da mutane a Najeriya
- Jami'an tsaro sun ceto mutane da aka yi garkuwa da su a Benue da Nasarawa, tare da kashe ’yan bindiga uku a fafatawar a Benue
- Haka zalika rundunar 'yan sanda ta kama makamai da alburusai, ciki har da bindigogi yayin ceto mutane a hannun 'yan ta'adda
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar ’yan sandan Najeriya ta bayyana cewa tana kara kaimi wajen dakile garkuwa da mutane da sauran laifuffuka a fadin kasar nan.
Rundunar ta samu nasarar ceto wani mutumi da aka yi garkuwa da shi a Kwande a jihar Benue, tare da kashe wasu ’yan bindiga uku.
Legit ta gano yadda aka fafata ne a cikin wani sako da rundunar 'yan sanda ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika an ruwaito cewa lamarin ya biyo bayan wani kiran gaggawa da aka yi wa sashen ’yan sanda na Vandiekya kan sace Tor Gajir da wasu ’yan bindiga suka yi.
Yadda aka fafata da yan ta'adda a Benue
Bayan jami’an tsaron sun samu bayanan sirri kan wani mutum mai suna Desmond Ahar, wanda aka zarga da hannu a sace Tor Gajir.
Bayan amsa tambayoyi, Desmond ya kai jami’an tsaron zuwa maboyar masu garkuwa da mutane a Adikpo, jihar Benue.
Yayin da suka isa maboyar, ’yan bindigar sun bude wuta kan jami’an tsaron, amma jami’an sun mayar da martani tare da kashe uku daga cikin ’yan bindigar, wasu sun tsere da raunukan harbi.
Tor Gajir ya samu kubuta ba tare da wani rauni ba, kuma an ba shi kulawa domin tabbatar da lafiyarsa. Haka kuma, jami’an tsaron sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu.
'Yan sanda sun ceto mutane a Nasarawa
A wani harin da aka kai a jihar Nasarawa ’yan sanda sun gano wata mota kirar Sienna da aka bari a kan hanyar Keffi zuwa Kaduna, kusa da kauyen Angwan Wayo.
Bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaron sun gano wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su, kuma ana ci gaba da neman masu garkuwa da mutanen.
Jami'an 'yan sanda sun kama makamai a Bayelsa
A ranar 7 ga Janairun 2025, jami’an ’yan sanda na jihar Bayelsa sun kama wani mai suna Usman Mohammed da ke hanyarsa ta zuwa jihar Rivers.
Bayan binciken motarsa, an gano bindiga kirar AK-47 guda daya, bindigar Type 09 AR guda daya, da kuma alburusai 120 da aka boye a cikin motar.
Shugaban 'yan sanda ya yabi jami’an tsaro
Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, ya yaba wa jami’an tsaron kan nasarorin da suka samu a Benue, Nasarawa, da Bayelsa.
IGP Kayode ya yi kira ga jami’an tsaron da su ci gaba da nuna kwazo wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.
Haka kuma, ya bukaci al’umma su kasance masu sa ido da goyon baya ga jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai kan duk wani motsin masu laifi.
Za a dakile 'yan bindiga masu kaura Kudu
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sun shirya tsaf domin dakile 'yan bindiga a Kudu.
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa za ta yi hadaka da 'ya banga, DSS da sauransu domin dakile 'yan bindiga masu hijira daga Kudu zuwa Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng