An Shirya Jami'an Tsaro tsaf domin Gwabzawa da 'Yan Bindiga Masu Komawa Kudu

An Shirya Jami'an Tsaro tsaf domin Gwabzawa da 'Yan Bindiga Masu Komawa Kudu

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi kira kan alamar shigowar ‘yan bindiga daga Arewa maso Yamma zuwa jiharsa a makon da ya wuce
  • Rundunar ‘yan sanda, 'yan bangar Amotekun, da kungiyar OPC sun ce suna kan shirin dakile yunkurin ‘yan bindigar na shiga jihohin Kudu
  • An ruwaito cewa jami’an tsaro sun dauki muhimman matakai daban-daban domin tabbatar da tsaro a jihohin Oyo, Ondo, Osun, Ekiti da kuma Ogun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Biyo bayan gargadin da gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi kan shigowar ‘yan bindiga daga Arewa zuwa jiharsa, jami’an tsaro na daukar matakan magance barazanar.

Rundunar ‘yan sanda, Amotekun, da kungiyar OPC sun ce za su yi aiki tare domin hana ‘yan bindigar samun mafaka a jihohin su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun dauko salon fadada ta'addanci zuwa Kudancin Najeriya

Yan sanda
An fara shirin hana 'yan bindiga shiga Kudancin Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A wata hira da Vanguard ta yi da manyan jami’an tsaro, sun bayyana irin matakan da suke dauka domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amotekun ta dauki matakai masu tsauri

Punch ta wallafa cewa jagoran Amotekun na Jihar Ondo, Cif Adetunji Adeleye, ya bayyana cewa sun tura jami’ai 1,200 zuwa kananan hukumomi 18 na jihar.

Adetunji Adeleye ya ce;

“Mun tsara dabaru tare da dukkan hukumomin tsaro a Jihar Ondo domin tabbatar da cewa ba za a sami wata kafa ga ‘yan bindiga ba.
Mun jajirce wajen tabbatar da tsaro a dukkan bangarorin jihar.”

A Jihar Osun, shugaban Amotekun, Adekunle Omoyele, ya ce suna maida hankali kan tattara bayanan sirri domin hana ta’addanci kamar garkuwa da mutane.

Amotekun
Dakarun Amotekun suna fareti. Hoto: Oyo State Government
Asali: Twitter

Jami’an tsaro za su hada kai

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Ondo, Wilfred Afolabi, ya ce suna aiki tare da Amotekun wajen kula da iyakokin jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

A cewarsa;

“Mun tanadi jami’an mu a iyakokin jihar. Za mu ci gaba da yin aiki kafada da kafada da Amotekun domin tabbatar da tsaron al’umma.”

A Jihar Oyo kuwa, kwamandan Amotekun, Kanal Bisiriyu Olayanju (mai ritaya), ya ce sun hada kai da sojoji, DSS, da kungiyoyin tsaro na gida domin karfafa tsaron iyakokin jihar.

Shirin da sauran gwamnonin jihohi suka yi

A Jihar Ekiti, mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro, Janar Ebenezer Ogundana (mai ritaya), ya ce an kara kaimi wajen sa ido kan duk wani motsi na ‘yan bindiga.

Ya bayyana cewa;

“Mun tanadi duk wani abu da za mu bukata domin tinkarar wannan matsala. An kuma tashi tsaye domin hana shigowarsu zuwa jihar mu.”

A Jihar Ogun, kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Ogunlowo, ya ce sun sanar da dukkan kwamandojin yankuna da DPO a jihar kan barazanar.

Kara karanta wannan

Ciyamomi 2 da yan majalisa sama da 10 sun fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Dukkan jami’an tsaro a jihohin da abin ya shafa sun tabbatar da cewa suna cikin shirin ko-ta-kwana domin dakile yunkurin ‘yan bindiga.

Ali Ndume ya karfafi jami'an tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ali Muhammad Ndume ya ziyarci dakarun rundunar Operation Hadin Kai a Maiduguri.

Ali Ndume ya ziyarci rundunar ne bayan sun yi wani kazamin fada da 'yan Boko Haram kuma suka kashe 'yan ta'addar kimanin 34.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng