Gwamna Abba Ya Yi Wa APC Martani Mai Zafi kan Shirin Karbe Kano a 2027
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi wa jam'iyyar APC wankin babban bargo kan yunƙurin da take yi na karɓe Kano a 2027
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ba zai amince da duk wani shirin yi wa mutanen Kano barazana ba, kuma a shirye yake ya ɗauki mataki
- Gwamnan Kano ya tunatar da ƴan adawan cewa mulki na Allah ne, kuma shi ne yake ba wanda ya so a kuma lokacin da ya so
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi martani ga jam'iyyar APC kan shirinta na karɓe mulkin Kano a shekarar 2027.
Gwamna Abba ya bayyana cewa gwamnatin jam’iyyar NNPP da ke mulki a jihar ba ta kallon APC wacce ta ƙwallafa ranta kan karɓe Kano a 2027 a matsayin barazana.
Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin rabon tallafin kuɗi na wata-wata ga mata 5,200 a fadar gwamnati da ke Kano, a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso ya tsokano APC
Idan ba a manta ba dai, ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce zai rage ƙuri’un APC a Kano a zaɓen 2027.
Amma a martanin da ya yi, daraktan yaɗa labarai na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya bayyana cewa NNPP ba barazana ba ce ga APC.
Kwanan nan, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce APC ita ce jam’iyyar da za ta ba abokan hamayyarta kashi a zaɓen 2027 a Kano.
Wane martani Gwamna Abba ya yi?
Amma a martanin da ya yi a jiya, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa mulki na Allah kuma shi ke ba da wa ga wanda ya so, a lokacin da ya so.
“Bari na faɗa cewa, duk wanda ya yi barazana ga mutanen Kano zai ɗanɗani kuɗarsa. A shirye muke, kuma ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin da ya dace a kansu."
“Game da waɗanda suke magana kan karɓe mulki a 2027, bari na tunatar da ku cewa mulki na Allah ne. Shi ne yake bai wa wanda ya ga dama, kuma muna addu’a Allah ya ba wa waɗanda suka fi ƙaunar ci gaban mutanen Kano."
“Mun yi imani da Allah, kuma mun san cewa ko da mutane nawa suka haɗu don su yaƙe mu, ba za su yi nasara ba idan Allah bai so hakan ba. Ba za mu ji tsoro ko fargaba ba."
"Burinmu ba ya kan 2027. Abin da muka fi maida hankali a kai shi ne sauke nauyin da mutanen Kano suka ba mu. Manufarmu ita ce ci gaba da samar da ribar dimokuraɗiyya da yi wa jama’armu aikin da ya dace."
"Muna roƙon Allah ya ba mu ƙarfi da ikon cimma wannan buri, da kuma ganin 2027 cikin ƙoshin lafiya."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya gargaɗi kwamishinoni
A wani labarin kuma, kun ji gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gayawa sababbin kwamishinonin da ya naɗa abin da ba zai lamunta ba a gwamnatinsa.
Gwamna Abba ya gargaɗe su kan cewa ba zai yarda da rashin biyayya ba da duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kawuna a majalisar zartarwar jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng