EFCC: Tsohon Gwamna Ya Shiga Matsala, Kotu Ta Kwace Masa Sama da N200m
- Kotun tarayya mai zama a Abuja ta amince da bukatar EFCC na kwace Naira miliyan 228.4 da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan Abia
- Mai shari'a Emeke Nwite ne ya yanke wannan hukunci bayan sauraron lauyan EFCC a shari'ar tsohon gwamna, Sanata Theodore Orji
- Alkalin ya kuma umarci a buga hukuncin kotun a kafafen watsa labarai domin ba da dama ga wanda ke ganin matakin bai dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin rufe asusu na wucin gadi tare da kwace Naira miliyan 228.4 da ke da alaƙa da tsohon gwamnan Abia, Sanata Theodore Orji.
Kotun ta ba da umarnin kwace kuɗin na wucin gadi tare da miƙawa gwamnatin tarayya kafin a kammala bincike kan yadda tsohon gwamnan ya mallake su.
Wannan hukunci ya zo ne a yayin da hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC ta taso Sanata Orji da bincike kan zargin almundahana da karkatar da kudade, Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta umarci kwace kudin na wucin gadi
Mai shari’a Emeka Nwite, wanda ya jagoranci zaman kotun ne ya bayar da wannan umarni bayan sauraron bukatar gaggawa da lauyan EFCC, Fadila Yusuf, ta gabatar.
Lauyan ta nemi kotun ta bayar da umarnin rufe asusun tare da kwace kudaden da aka gano a hannun kamfanin Effdee Nigeria Ltd.
Alkalin kotun ya kuma umarci EFCC ta wallafa umarnin a shafin yanar gizon hukumar da kuma jaridar Daily Trust domin sanar da jama'a matakin kwace kudin.
Wannan mataki na nufin bai wa duk wani mai alaƙa da kudaden damar bayyana gaban kotu cikin kwanaki 14 domin gabatar da hujjojinsa.
Dalilin kwace kudaden a shari'ar tsohon gwamna
Bisa ga bayanan EFCC, kudaden da ake magana a kansu suna karkashin bincike kan yadda aka same su da kuma wadanda suka mallake su.
Lauyan hukumar EFCC ta bayyana cewa an gano kudaden a wani asusu na kamfanin Effdee Nigeria Ltd a bankin Keystone.
Kotun ta yi hukunci ne bisa tanadin sashe na 44(2)b) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da sashe na 17 na dokar yaƙi da zamba da manyan laifuka ta 2006.
Siyasar Sanata Theodor Orji
Sanata Theodore Orji ya shugabanci jihar Abia a matsayin gwamna daga 2007 zuwa 2015.
Bayan kammala wa’adin mulkinsa a matsayin gwamna, ya zama sanata mai wakiltar Yankin Abia ta Tsakiya a Majalisar dattawa, ya yi wa’adi biyu kafin ya yi ritaya daga siyasa.
Alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2025, domin bayar da rahoton yadda aka cika umarnin kotun da kuma ci gaba da sauraron shari'ar.
Kotu ta amince EFCC ta rufe asusu 24
A wani labarin, kun ji cewa kotu ta amincewa hukumar EFCC ta garƙame wasu asusun banki 24 bisa zargin alakarsu da ayyukan ɗaukar nauyin ta'addanci.
Kotun ta bai wa hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC wa'adin watanni uku ta kammala bincike kan asusun na wani da ake zargi da garkuwa da mutane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng