'Mun Fi Ku Saninsu': Basarake Ya Roki Gwamnati Alfarma kan Al'umma, Ya Jero Dalilai
- Sarkin Lokoja, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi IV, ya bukaci gwamnati ta bai wa sarakuna mukamai saboda kusancinsu da al'umma
- Sarkin ya ce salon jagorancinsa ya taimaka masa wajen fahimtar matsalolin jama'a, ya kuma ziyarci asibitoci don tallafa wa marasa lafiya
- Ya ce akwai darussan da ya koya a rayuwarsa tun bayan darewa karagar mulki na sarautar Lokoja inda ya ba masu hannu da shuni shawara
- Basaraken ya yaba wa Gwamna Ododo bisa kyawawan ayyukan cigaba da kulawa da jin dadin jama'a tare da kiran ci gaba da kusantar jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Lokoja, Kogi - Sarkin Lokoja a jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Gambo Kabir Maikarfi IV, ya ce akwai bukatar gwamnati ta bai wa sarakuna mukamai saboda kusancinsu da talakawa.
Basaraken ya bayyana tasirin sarakunan gargajiya musamman wurin daidaita lamura a cikin al'umma da kuma ɓangaren samar da tsaro.
Basarake ya fadi rawar da suke takawa
A cewarsa, matsayin da yake na sarki ya ba shi damar samun labari kai tsaye daga jama'a game da matsalolinsu kafin gwamnati ta sani, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya ce sarakuna suna da rawar gani wajen kare al'adun al'umma da al'adar gargajiya, wanda ke taimakawa wajen cigaban rayuwar jama'a.
Alhaji Ibrahim ya bayyana matsayin Maigarin Lokoja a matsayin babban nauyi, amma ya ce ya samu ilimi daga kakanni da mahaifansa da suka taba mulki.
Sarki ya fadi irin gogewar da yake da shi
"Gogewata da aikin da na yi a wurare daban-daban sun saukaka mani jagorancin jama'a."
"Na tarar da yanayi mai ban tsoro a asibitin koyarwa, ya kamata jama'a su taimaka wa mabukata don kyautata rayuwa."
- Alhaji Ibrahim Gambo Kabir
Sarkin ya bukaci masu hannu da shuni da su tabbatar da sun cigaba da ba mabukata tallafi saboda halin da ake ciki.
Basarake ya ba da shawara kan shugabanci nagari
A cewarsa, bambancin addini ko kabilanci bai kamata ya zama shinge ga shugabanci ba, inda ya nuna muhimmancin karbar kowa da kowa.
Ya ce samun shugabanci nagari shi ne abu mafi muhimmanci ga kowace al'umma da ke fatan samun wakilci ba tare da yin nadama ba.
Yayin cika shekara guda a karagar mulki, Maigarin ya ziyarci asibitoci, ya tallafa wa marasa lafiya da bayar da magunguna da biyan kudin asibiti.
Gwamna da mai gidansa sun barke da rawa
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya ba da nishaɗi a fadar mai martaba sarkin Ebira watau Ohinoi na Ebiraland da ke jihar a makon da ya gabata.
A wani faifan bidiyo da ke yawo an ga Yahaya Bello tare da Gwamna Mohammed Usman Ododo suna tiƙar rawa cikin farin ciki a gaban basaraken ba tare da jin kunya ba.
Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya samu ƴanci daga gidan yarin Kuje a birnin Tarayya Abuja sakamakon cika sharuɗɗan belin da kotu ta ba shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng