Ndume Ya Yi Goma Ta Arziki ga Mutanen Borno da Harin Boko Haram Ya Shafa
- Ali Ndume ya ziyarci hedkwatar rundunar Operation Hadin Kai domin yaba wa jaruman sojoji bisa kokarinsu na yakar ‘yan ta’adda
- Sanata Ndume ya jajenta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin da aka kai Sabon Gari, Damboa, a ranar Asabar da ta gabata
- 'Dan majalisar ya bayar da tallafi ga wadanda harin ya rutsa da su, tare da yin kira da a ci gaba da bayar da goyon baya ga dakarun sojoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Ali Ndume, ya ziyarci hedkwatar rundunar sojin Najeriya ta Operation Hadin Kai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a ranar Talata.
Sanatan ya kai ziyarar ne domin jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin Boko Haram da aka kai a kauyen Sabon Gari na karamar hukumar Damboa.
Leadership ta rahoto cewa Ali Ndume ya yaba wa sojojin bisa jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka ji rauni a harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin Ali Ndume ga sojojin Najeriya
Sanata Ndume ya yi amfani da damar ziyarar wajen yabon kokarin sojoji na yakar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas.
Sanatan ya ce:
“Na gode sosai da jajircewar ku da sadaukarwar ku wajen kare al’ummarmu. Jarumtakarku abin yabo ce, kuma za mu ci gaba da kasancewa tare da ku.”
Bayan haka, ya gana da wadanda harin ya rutsa da su, inda ya nuna tausayi tare da bayar da gudunmawa ta kudi da karfafa musu gwiwa.
Rundunar tsaro ta fitar da sanarwa kan yadda sojoji suka dakile wani mummunan hari na Boko Haram/ISWAP a Sabon Gari.
Sanarwar ta kara da cewa, sojojin sama da na kasa sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 34 a artabun, amma, abin takaici, sojoji shida sun rasa rayukansu.
Kalubalen tsaro a Kudancin jihar Borno
Kudancin Borno, musamman wurare kamar Dutsen Mandara, Damboa, Biu Mandaga Garau, da wasu sassa na Ngulde da Ngwahi a Askira/Uba, na fuskantar matsalolin tsaro masu tsanani.
Tribune ta wallafa cewa Sanata Ndume ya saka labule da kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Waidi Shuaibu a lokacin ziyarar.
Ganawar tasu ba za ta rasa nasaba da hare-haren da suka faru ba, ciki har da na Kauji, Wajirko, da Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, wacce ke cikin mazabarsa.
“Ba za mu taba manta sadaukarwarku ba wajen tabbatar da tsaron al’ummarmu. Dole ne mu ci gaba da marawa rundunar sojoji baya domin samun nasarar murkushe ‘yan ta’adda.”
- Ali Ndume
Nuna goyon baya da kira ga jama’a
Sanata Ndume ya kuma yi kira ga daukacin al’umma da su hada kai da gwamnati wajen ba da goyon baya ga sojoji domin kawo karshen ta’addanci a yankin.
“Duk da irin kalubalen da muke fuskanta, ya zama wajibi a gare mu da mu ci gaba da goyon bayan sojoji. Wannan yaki na kowa ne, kuma in Allah ya yarda, za mu yi nasara.”
- Ali Ndume
'Yan bindiga sun kashe 'ya'yan boka
A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ake zaton 'yan bindiga ne sun haura gidan wani boka sun yi masa barna a jihar Anambra.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen sun kashe 'ya'yan bokan uku kuma 'yan sanda sun fara bincike domin gano inda miyagun suka buya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng