'Magana Ta Fara Fitowa': Hamza Al Mustapha Ya Fadi Dalilin Ganawa da El Rufa'i

'Magana Ta Fara Fitowa': Hamza Al Mustapha Ya Fadi Dalilin Ganawa da El Rufa'i

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana takaicin yadda aka yi watsi da talakawa
  • Al-Mustapha ya ce har yanzu ba a gama fahimtar irin barnar da aka yi wa rayuwar 'yan Najeriya ba, sai a nan gaba
  • Ya kara da bayyana cewa haduwarsu da Nasir El-Rufa’i da jagororin SDP ta biyo bayan damuwar halin da Najeriya ke ciki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon dan takara Shugaban kasa, Manjo Hamza Al Mustapha (rtd) ya bayyana takaicin halin da shugabannin Najeriya su ka jefa talakawa.

Al Mustapha ya na wannan bayani ne jim kadan bayan an gano shi ya gana da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i yayin da ake rade-radin haɗaka.

Kara karanta wannan

Ana hasashen hadakar adawa, El Rufai ya gana da Hamza Al Mustapha da jigon PDP

Segun
Al Mustapha ya fadi abin da ya tattauna da El Rufa'i Hoto: @SegunShowunmi
Asali: Twitter

A bidiyon da DCL Hausa ta wallafa a shafin Facebook, tsohon dogarin Shugaban kasar nan ya ce shugabanni sun riga sun cuci talakawan da su ke mulka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya koka bisa abin da ya kira da cewa an yi wa talaka aringizo, kuma har yanzu ba a kai ga gama gano irin illar da aka yi wa rayuwar mutanen Najeriya ba.

"Shugabanni sun yi watsi da talaka," Al-Mustapha

Daya daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa a zaben da ya gabata, Hamza Al Mustapha ya ce wasu daga cikin shugabanni ba su damu da halin da talakawa ke ciki ba.

Ya bayyana cewa;

"Masu ilimin ma da yawa ba su san irin ta'adin da aka yi wa kasa ba, sai nan gaba za su fahimta. Wanda su ke da akwai, wanda su ke zama a Abuja, in ka gaya masu haka, sai su ga kamar almara ne."

Kara karanta wannan

APC: El Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan jita jitar sauya sheka

Ba su san halin da mutane su ke ciki ba, in za su je wuri, sai dai su shiga jirgin sama, in sun je a tarbe su da kide-kide, su watsa kudi ba girma.

Al-Mustapha: Dalilin ganawa da El Rufa'i

Manjo Hamza Al Mustapha ya ce masu kishin kasa da fafutukar nemo mafita daga cikin mawuyacin halin da ake ciki ne su ka hadu domin tattaunawa matsalolin.

Ya kara da cewa;

Haduwa ce aka yi saboda damuwa da yadda Najeriya ta ke ciki. Shi Shugaban jam'iyya na SDP ya ke dubawa babu maganar jam'iyya.

Ya ce jagorancin SDP da Nasir El Rufa'i sun tattauna makomar kasar nan, da ma inda za su dosa domin a samu ciccibo ta daga halin da ta ke ciki.

El Rufa'i, Al Mustapha sun sa labule

A wani labarin, kun ji cewa a yayin da hasashen kafa hadakar jam’iyyun adawa ke kara karfi a Najeriya, tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gana da wasu jiga-jigai.

Kara karanta wannan

'Na san za a zage ni': Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya

Tsohon gwamnan ya gana da manyan ‘yan siyasa a birnin tarayya Abuja su ka da tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.