APC Ta Yi Martani bayan ba Tinubu Lamba Ta 3 a Rashawa a Duniya

APC Ta Yi Martani bayan ba Tinubu Lamba Ta 3 a Rashawa a Duniya

  • APC ta reshen kasar Amurka ta kare Bola Ahmed Tinubu daga zarge-zargen rashawa, jabun takardun karatu da alaka da miyagun kwayoyi
  • Shugaban APC na kasar Amurka, Farfesa Tai Balofin, ya yi kira da a daina yada maganganun da ba su da tushe domin bata sunan Tinubu
  • Farfesa Balofin ya bayyana zarge-zargen da aka yi wa Tinubu a matsayin makarkashiya da ke nufin bata mutuncin Najeriya da shugabancinta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC reshen Amurka ta yi Allah-wadai da zarge-zargen da ake wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa hakan ba zai kawo ci gaban Najeriya ba.

Shugaban reshen jam’iyyar, Farfesa Tai Balofin, ya bayyana cewa zarge-zargen rashawa, jabun takardun karatu, da alaka da miyagun kwayoyi da ake wa Bola Tinubu ba su da tushe.

Kara karanta wannan

Shugaban Ghana ya jefa mutanen duniya a mamaki wajen kiran Tinubu a taro

Ganduje
APC ta yi martani kan zargin Tinubu da rashawa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Leadership ta wallafa cewa Farfesa Balofin ya yi kira da a daina yada maganganun da za su kawo rarrabuwar kawuna, maimakon haka a hada kai domin ciyar da Najeriya gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin APC kan zargin shugaba Tinubu

The Guardian ta wallafa cewa Farfesa Balofin ya bayyana cewa zarge-zargen da aka yi wa Shugaba Tinubu ba su da wani dalili mai karfi.

Farfesa Balofin ya ce;

“Wannan lokaci ne da ya kamata ‘yan Najeriya su mayar da hankali kan sukar da za ta kawo gyara,
"Ba irin wadannan zarge-zargen da ba su da tushe ba, da nufin neman suna marar amfani.”

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa game da lambar cin hanci da rashawa da kungiyar OCCRP ta ba wa Tinubu.

Legit ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana Bola Tinubu a matsayin daya daga cikin mutanen da suka fi rashawa a duniya a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dakatar da sarki da majalisarsa bayan korafin jama'a

Balofin ya bayyana lamarin a matsayin makarkashiya domin haddasa rashin hadin kai da fitina tsakanin ‘yan Najeriya.

Kare mutuncin Najeriya a matakin duniya

Shugaban APC reshen Amurka ya bayyana cewa hukumomin Amurka sun wanke shugaba Tinubu daga irin wadannan zarge-zarge.

“Akwai bukatar tunawa masu yada wannan labarin cewa hukumomin Amurka sun tabbatar da cewa Tinubu ba shi da alaka da wadannan zarge-zargen.
"Dawo da batun da aka wanke tun farko yana iya jawo suka ga mutuncin shugabancin Najeriya da matsayin kasar a duniya.”

- Farfesa Balofin

Balofin ya yi kira ga kungiyoyin da ke yada irin wadannan labarai su janye kalaman da suka yi wa Tinubu.

'Tinubu zai cigaba da kokari' - APC

Balofin ya ce shugaba Tinubu na da hangen nesa mai zurfi kuma zai cigaba da jagorantar Najeriya da kwazo duk da zarge-zargen da ake masa.

Jam’iyyar APC reshen Amurka ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su hade kai don taimaka wa Shugaba Tinubu wajen fitar da Najeriya daga kangin koma baya.

Kara karanta wannan

LND: Ana shirin kafa sabuwar jam'iyya domin buga APC da kasa a 2027

Dalung ya yi magana kan mulkin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya ce akwai wasu mutane masu hadari da suka kewaye Bola Tinubu.

Solomon Dalung ya bayyana cewa hakan ya faru a lokacin tsohon shugaba Buhari amma 'yan-ba-ni-na-iya a mulkin Tinubu sun fi hadari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng