Majalisa Ta Fara Nazarin Kasafin Kudin N49tr, Za a Tsefe Bukatun Gwamnatin Tinubu

Majalisa Ta Fara Nazarin Kasafin Kudin N49tr, Za a Tsefe Bukatun Gwamnatin Tinubu

  • Majalisar wakilan tarayya ta ce ana cikakken nazari kan kasafin kudin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar
  • Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 49.74 a ranar 18 Disamba, 2024 a gaban zaman majalisa na hadin gwiwa
  • Mataimakin mai magana da yawun majalisar, Philip Agbese, ya bayyana cewa za su zauna domin duba kowane sashe na kasafin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Majalisar Wakilan Najeriya ta bayyana cewa za ta yi cikakken nazari kan kasafin kudi na 2025 da a yanzu haka ke gabanta.

Mataimakin mai magana da yawun majalisar, Philip Agbese, ya bayyana hakan a ranar Talata, yana mai ba da tabbacin cewa majalisar za ta yi aiki kan kasafin domin ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Majalisa
Majalisa ta fara duba kasafin kudin 2025 Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar 18 Disamba, 2024, ya gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 49.74.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan gabatar da kasafin a zaman hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Kasa, Shugaba Tinubu ya nemi a gaggauta dubawa da amincewa da shi.

Majalisa ta fara aiki a kan kasafin kudin 2025

Da zantawarsa da manema labarai a Abuja, Mataimakin mai magana da yawun majalisar, Philip Agbese ya ce 'yan majalisa za su tattara hankalinsu a kan kasa.

Ya kara da cewa:

"Aikin bangaren zartarwa ne gabatar da kasafin kudi, amma a matsayinmu na bangaren majalisa mai zaman kanta, za mu yi aikinsa yadda ya dace.
“Kamar yadda muka yi a shekarar 2024, za mu tsaya kan bukatun kasa wajen kai wa ga kudurin karshe da za mu amince da shi tare da tura wa Shugaban Kasa don rattaba hannu.”

Kara karanta wannan

"An shiga wahala bayan zaben Tinubu," Sanatan APC ya fadi manufar gwamnati

Majalisa ta damu da walwalar jama'a

Mista Agbese ya ce Majalisar Wakilai ta 10 karkashin jagorancin Kakakin Majalisa, Tajudeen Abbas, ta jajirce wajen inganta walwalar ’yan Najeriya.

Ya kara da bayyana yadda 'yan majalisa su ke da kishin 'yan Najeriya, da kokarin da za su yi wajen tabbatar da kasafin ya taba bangarorin da za su amfane su.

Ya ce;

“A matsayinta na majalisa, ba mu da wani buri face kare muradun kasa. Abin da muke so kawai shi ne alherin kasar mu da mutanen mu.
Don haka, yayin da muke kan wannan muhimmin aikin, za mu duba bangarorin tattalin arziki da ke da damar bunkasa ci gaban kasa, sannan mu dauki matakin da ya dace.”

Ana lallaba dan majalisa kan kudirin haraji

A baya, kun ji cewa dan majalisar NNPP, Dr. Mustapha Ghali ya bayyana yadda ake kokarin shawo kansa domin amincewa da kudirin harajin gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

Hon. Ghali, wanda ya fadi haka yayin zantawarsa da manema labarai a jihar Kano, ya na daga cikin masu tsatstsauran adawa da kudirorin gyaran harajin Bola Tinubu.

Dan Majalisar ya kafe a kan matsayarsa na gabatar da kudirin a wannan lokaci, inda ya ce 'yan Najeriya su ma fama da matsalolin da zai hana su jin dadin sabon tsarin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.