"Mun Kashe Yan Ta'adda 34," DHQ Ta Yi Magana kan Harin da Aka Kai Sansanin Sojoji
- Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin haske kan harin da mayaƙan ISWAP suka yi yunkurin kai wa sansanin sojoji a jihar Borno
- Kakakin DHQ na ƙasa,Janar Edward Buba ya ce sojoji sun yi nasarar daƙile ƴan ta'addan tun kafin su ida nufinsu a sansanin da ke Sabon Gari
- Buba ya tabbatar da cewa an kashe ƴan ta'adda 34, dakarun soji 6 sun rasa ransu yayin musayar wuta da maharan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta yi bayanin abin da ya fari lokacin da mayakan kungiyar ta'addancin ISWAP suka farmaki sansanin sojojin Najeriya a Borno.
DHQ ta ce 'yan ta'adda 34 da sojoji shida sun rasa rayukansu a harin da aka kai sansanin sojoji da ke Sabon Gari, karamar hukumar Damboa a jihar Borno.
Daraktan yada labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a halin yanzu ba za a bayyana sunayen sojojin da suka rasa rayukansu ba domin ba wa hukumar soji damar sanar da iyalansu, rahoton Daily Trust.
Dakarun sojoji sun tari ƴan ta'adda a Borno
A cewar Manjo Janar Buba, 'yan ta'addan sun yi yunkurin kai wa sojojin hari don ramuwar gayya kan kashe kwamandansu da wasu mayaka da sojoji suka yi kwanan nan.
Ya ce ƴan ta'addan sun sha mamaki yayin da dakarun sojojin da ke dawowa daga sintiri suka tarbe su, wanda hakan ya ba sojojin da ke sansani damar yin shiri cikin lokaci.
Buba ya ce da zuwan ƙarin tawagar sojoji da jami'an tsaro wanda suka ƙunshi dakarun rundunar CJTF, ƴan sa'kai, da sauransu, ya ƙara masu ƙarfin fatattakar maharan.
Ƴan ta'addan sun dasa nakiya a hanya
Kakakin DHQ ya ce duk da cewa tawagar sojojin sun gamu da wata nakiya da aka dasa a hanya, wadda ta ji wa kwamandan 'yan sa-kai rauni, sun isa wurin cikin lokaci kuma sun tarwatsa 'yan ta'addan da ke guduwa.
Ya kara da cewa sashen rundunar sojin sama na Operation Haɗin Kai ya sake tarfa ƴan ta'addan da ruwan bama-bamai ta sama a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa.
DHQ ta ce sojoji sun kashe ƴan ta'adda 34
A cewarsa, binciken barnar yaki watau BDA ya nuna cewa sojojin sun kashe 'yan ta'adda da dama kuma sun kwato makamai.
“A jimilla, an kashe 'yan ta'adda 34, sannan an kwato bindigogi 23 kirar AK47. Haka kuma, sojoji sun kwato harsasai sama da 200. Abin takaici, mun rasa dakaru 6,” in ji shi.
Edward Buba ya sake jaddada cewa rundunar sojin Najeriya ta san nauyi da alhakin da ke kanta na kawo karshen ta’addanci da tayar da kayar baya a kasar nan.
Sojoji sun murƙushe miyagu a Ribas
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta hallaka tawagar ƴan ta'addan da suka faramki sojoji a jihar Ribas.
An ruwaito cewa da farko an kama ƴan ta'adda, amma da suka yi yunƙurin guduwa sojoji suka harbe su har lahira.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng